Gabatarwar Sashe na 10
Jehobah shi ne Sarkin duniya gabaki ɗaya. Shi ne yake iko kuma zai ci gaba da kasancewa da iko. Alal misali, ya ceci Irmiya daga wata rijiyar da aka jefa shi ciki don ya mutu. Ya ceci Shadrach da Meshach da kuma Abednego daga wuta mai zafi. Ya kuma ceci Daniyel daga hannun zakuna. Jehobah ya kāre Esther don ta iya ceton mutanenta. Ba zai bar mutane su ci gaba da yin mugunta har abada ba. Annabcin da aka yi game da babban gunki da kuma bishiya sun nuna cewa Mulkin Jehobah zai mulki duniyar nan kuma zai cire mugunta gabaki ɗaya.