Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • hf sashe na 7 pp. 22-25
  • Yadda Za Ku Koyar da ’Ya’yanku

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Ku Koyar da ’Ya’yanku
  • Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • 1 KADA KU SA YARANKU SU JI TSORON TATTAUNAWA DA KU
  • 2 KU YI ƘOƘARI KU FAHIMCI ABIN DA SUKE NUFI
  • 3 KU KASANCE DA HAƊIN KAI
  • 4 KU KASANCE DA TSARI
  • Iyaye, Ku Koyar Da ’Ya’yanku Cikin Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Gina Iyali Mai Ƙarfi A Ruhaniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ku Koya Wa Yaranku Su Ƙaunaci Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Mene ne Zai Sa Iyaye da Yara Farin Ciki?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
hf sashe na 7 pp. 22-25
Baba da yaro suna gyaran keke tare

SASHE NA 7

Yadda Za Ku Koyar da ’Ya’yanku

“Waɗannan zantattuka fa, da ni ke umurce ka yau, za su zauna cikin zuciyarka: kuma za ka koya wa ’ya’yanka su da anniya.”—Kubawar Shari’a 6:6, 7

A lokacin da Jehobah ya tsara yadda iyali za ta kasance, ya ba iyaye hakkin kula da ’ya’yansu. (Kolosiyawa 3:20) A matsayinku na iyaye, hakkinku ne ku yi rainon ’ya’yanku don su ƙaunaci Jehobah kuma su zama mutanen kirki. (2 Timotawus 1:5; 3:15) Wajibi ne ku yi ƙoƙari ku san abin da ke cikin zuciyar ’ya’yanku. A gaskiya, yana da muhimmanci ku kafa musu misali mai kyau. Dole Kalmar Jehobah ta kasance a zuciyarku kafin ku koya wa ’ya’yanku ita sosai.​—Zabura 40:8.

1 KADA KU SA YARANKU SU JI TSORON TATTAUNAWA DA KU

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: ‘Ku yi hanzarin ji, ku yi jinkirin yin magana.’ (Yaƙub 1:19) Kuna so yaranku su riƙa tattaunawa da ku. Saboda haka, ku nuna musu cewa za ku saurare su a duk lokacin da suke so su tattauna da ku. Idan kuna so su gaya muku abin da ke zuciyarsu, kada ku hau su da faɗa. (Yaƙub 3:18) Idan suna ganin ku masu zafin hali ko kuma masu kushe mutane, ba za su so su gaya muku abin da ke zuciyarsu ba. Ku bi da ’ya’yanku cikin haƙuri kuma ku riƙa nuna musu cewa kuna ƙaunarsu.​—Matta 3:17; 1 Korintiyawa 8:1.

SHAWARA:

  • Ku saurara idan yaranku suna so su tattauna da ku

  • Ku riƙa tattaunawa da ’ya’yanku a kai a kai, ba sai suna da damuwa ba

2 KU YI ƘOƘARI KU FAHIMCI ABIN DA SUKE NUFI

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Kowane mutum mai-hankali ya kan yi aikinsa bisa ga ilimi.” (Misalai 13:16) A wasu lokatai, kuna bukatar ku yi nazarin kalmomin da yaranku suka gaya muku don ku fahimci ainihin abin da ke damunsu. Matasa suna yawan ƙara gishiri ko kuma su faɗi abin da ba ya zuciyarsu. Kalmar Allah ta ce: “Wanda ya mayar da magana tun ba ya ji ba, wauta ce gare shi da kunya.” (Misalai 18:13) Saboda haka, kada ku yi saurin fushi da su.​—Misalai 19:11.

Uwa tana fushin abin da yarinyarta ta fada

SHAWARA:

  • Ku ƙudura cewa ba za ku katse wa yaranku magana ba ko kuma ku yi saurin ɗaukan mataki, ko da mene ne suka faɗa

  • Ku tuna da yadda ku ma kuka ji sa’ad da kuke yara da kuma abin da ya fi muku muhimmanci a lokacin

3 KU KASANCE DA HAƊIN KAI

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Ɗana, ka ji koyarwar ubanka, dokar uwarka kuma kada ka yar da ita.” (Misalai 1:8) Jehobah ya ba iyaye iko bisa yaransu. Wajibi ne ku koya wa yaranku yadda za su girmama ku kuma su yi muku biyayya. (Afisawa 6:1-3) A duk lokacin da iyaye ba su kasance da “nufi ɗaya” ko kuma haɗin kai ba, yaransu za su gano hakan. (1 Korintiyawa 1:10, Littafi Mai Tsarki) Idan ya faru cewa ra’ayinku ya saɓa a batun raino, kada ku nuna musu hakan domin za su rena ku.

Wani uba ya shigar da dansa daki shi kadai don ya yi masa horo ba a gaban kaninsa da uwarsa ba

SHAWARA:

  • Ku tsai da shawara a kan yadda za ku riƙa yi wa yaranku horo

  • Idan ra’ayinku a kan yadda za ku hori yaranku bai zo ɗaya ba, ku yi ƙoƙari ku fahimci juna

4 KU KASANCE DA TSARI

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Ka goyi [‘yi rainon,’ NW] yaro cikin hanya da za shi bi.” (Misalai 22:6) Yaranku ba za su kasance da tarbiyya mai kyau haka kwatsam ba. Wajibi ne ku tsara yadda za ku koyar da su, kuma wannan tsarin ya haɗa da yin horo. (Zabura 127:4; Misalai 29:17) Ba yi wa yaro duka ne kawai horo ba, amma horo ya ƙunshi taimaka masa ya fahimci muhimmancin umurnin da aka ba shi. (Misalai 1:5) Ƙari ga haka, ku taimaka wa yaranku su so Kalmar Allah kuma su fahimci ƙa’idodin da ke cikinta. (Zabura 1:2) Hakan zai taimaka musu su kasance da lamiri mai kyau.​—Ibraniyawa 5:14.

SHAWARA:

  • Ka taimaki yaranka su ɗauki Jehobah a matsayin Wanda ya wanzu da gaske kuma za su iya dogara da shi

  • Ka taimaka musu su guji abubuwan da za su iya ɓata ɗabi’arsu, kamar waɗanda ke Intane da kuma dandalin sada zumunta. Ku koya musu yadda za su guji masu yin lalata da yara

Iyaye suna koya wa dansu yadda zai yi ibada ga Jehobah tun yana karami har ya kai lokacin da zai yi baftisma

‘Ka yi rainon yaro cikin hanya da za shi bi’

JEHOBAH ZAI ALBARKACI ƘOƘARINKU

A matsayinku na iyaye, Jehobah ya ba ku aiki na musamman, wato koya wa yaranku umurninsa. (Afisawa 6:4) Jehobah ya san cewa yin hakan ba ƙaramin aiki ba ne, amma ku san cewa ƙoƙarin da kuke yi zai kawo yabo ga Allah kuma zai sa ku farin ciki.​.—Misalai 23:24.

KA TAMBAYI KANKA . . .

  • Ta yaya zan sa yarana su rika gaya mini abin da ke zuciyarsu?

  • Mene ne zan koya daga yadda wasu iyaye suke rainon ’ya’yansu?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba