Mene Ne Ra’ayinka Game Da Littafi Mai Tsarki?
Kana ganin . . .
littafi ne da ke ɗaukaka ra’ayin ’yan Adam?
littafin tatsuniya ne da kuma ƙage?
Kalmar Allah ce?
ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE
‘Kowane nassi hurarre ne daga wurin Allah.’—2 Timotawus 3:16, Littafi Mai Tsarki.
ABIN DA ZA KA IYA MORA IDAN KA GASKATA DA HAKAN
Za ka sami tabbataccen amsoshi ga tambayoyi masu muhimmanci a rayuwa.—Misalai 2:1-5.
Za ka sami ja-gora mai kyau a rayuwarka ta yau da kullum.—Zabura 119:105.
Za ka kasance da tabbataccen bege game da nan gaba.—Romawa 15:4.
ZA MU IYA GASKATA DA LITTAFI MAI TSARKI KUWA?
Hakika, aƙalla saboda waɗannan dalilai uku:
Jituwa. Mutane 40 ne suka rubuta Littafi Mai Tsarki a lokatai dabam-dabam kuma hakan ya ɗauki shekaru 1,600. Yawancin su ba su san juna ba. Duk da haka, babu saɓani a abubuwan da suka rubuta a cikin littafin, ƙari ga haka, yana ɗaukaka sunan Allah da kuma mulkinsa!
Tabbataccen tarihi. Masana tarihi suna yawan rufa-rufa sa’ad da aka ci mutanensu a yaƙi. Akasin haka, marubutan Littafi Mai Tsarki sun bayyana kurakuransu da na mutanensu a fili.—2 Labarbaru 36:15, 16; Zabura 51:1-4.
Annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki suna cika tabbas. Littafi Mai Tsarki ya yi annabci cewa za a halaka birnin Babila na dā shekaru 200 kafin hakan ya auku. (Ishaya 13:17-22) Ya bayyana yadda za a halaka Babila har da sunan wanda zai ci birnin da yaƙi!—Ishaya 45:1-3.
Haka ma, wasu annabce-annabce da dama a cikin Littafi Mai Tsarki sun cika daidai yadda aka ambata. Hakika, haka ya kamata Kalmar Allah ta kasance, ko ba haka ba?—2 Bitrus 1:21.
KA YI TUNANI A KAN WANNAN TAMBAYAR
Ta yaya Kalmar Allah za ta inganta rayuwarka?
Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar a ISHAYA 48:17, 18 da kuma 2 TIMOTAWUS 3:16, 17.