Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • jl darasi na 28
  • Waɗanne Bayanai Ne Za Ka Iya Samu a Yanar Gizonmu?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Waɗanne Bayanai Ne Za Ka Iya Samu a Yanar Gizonmu?
  • Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
  • Makamantan Littattafai
  • A Ina Ne Za Mu Sami Amsoshin Muhimman Tambayoyi?
    A Ina Ne Za Mu Sami Amsoshin Muhimman Tambayoyi?
  • Dandalinmu na Intane—Ku Yi Amfani da Shi Wajen Yin Nazari da Iyalinku ko Kuma Ku Kaɗai
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Dandalinmu na Intane—Ku Yi Amfani da Shi Sa’ad da Kuke Wa’azi
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Ku Yi Amfani da Shafin Farko na JW.ORG Yayin da Kuke Waꞌazi
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
Dubi Ƙari
Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
jl darasi na 28

DARASI NA 28

Waɗanne Bayanai Ne Za Ka Iya Samu a Yanar Gizonmu?

Wata mata tana bincike a kwamfutar tafi da gidanka

Faransa

Wata iyalin tana amfani da kwamfuta

Poland

Wata mata tana kallon bidiyon kurame a dandalinmu

Rasha

Yesu Kristi ya gaya wa mabiyansa: “Ku bari haskenku shi haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu-kyau, su girmama Ubanku wanda ke cikin sama.” (Matta 5:16) Shi ya sa muke amfani sosai da fasaha ta zamani, har da Intane. Yanar Gizonmu, jw.org ne ainihin dandanlin da za a iya samun bayanai game da imani da kuma ayyukan Shaidun Jehobah. Waɗanne abubuwa ne za a iya samu a dandalin?

Amsoshi daga Littafi Mai Tsarki na tambayoyin da mutane suke yi a yau da kullum. Za ka iya samun amsoshin tambayoyi masu muhimmanci waɗanda mutane suka taɓa yi. Alal misali, za a iya samun warƙoƙin nan Wahala Za Ta Kare Kuwa? da kuma Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa? a harsuna sama da 600 a dandalinmu. Za ka samu fassarar Littafi Mai Tsarki na New World Translation of the Holy Scriptures a harsuna sama da 130 da kuma littattafan da suka bayyana Littafi Mai Tsarki, har da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? tare da Hasumiyar Tsaro da Awake! na kwanan nan. Za a iya karanta ko kuma a saurari karatun da dama daga cikin waɗannan littattafan ta hanyar Intane ko kuma a MP3 ko PDF ko kuma EPUB. Kana iya buga wasu shafuffuka don ka nuna wa mutumin da ke son gaskiya a harshensa! Ana samun bidiyo a yaren kurame da dama. Za ka iya sauko da wasan kwaikwayon da aka ɗauko daga Littafi Mai Tsarki, da kuma waƙoƙi masu daɗi.

Bayani na gaskiya game da Shaidun Jehobah. Har ila, akwai labarai da ɗimi-ɗiminsu tare da bidiyo game da aikinmu a faɗin duniya, da abubuwan da suke shafan Shaidun Jehobah da kuma ƙoƙarin da muke yi don mu taimaka wa waɗanda bala’i ya shafa. Za ka iya samun bayani game da taron gundumarmu da ke tafe da kuma adireshin ofisoshinmu na reshe.

Ta waɗannan hanyoyin ne muke haskaka gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki a duk faɗin duniya. Mutane a dukan nahiyoyin duniya, har da Antarctica, suna amfana daga wannan shirin. Fatarmu ita ce ‘maganar Ubangiji ta ci gaba da yaɗuwa da sauri’ a faɗin duniya, kuma ɗaukaka ta kasance ga Allah.—2 Tasalunikawa 3:1.

  • Ta yaya jw.org yake taimaka wa mutane da yawa su koyi gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki?

  • Mene ne za ka so ka bincika a Yanar gizonmu?

GARGAƊI:

’Yan hamayya suna amfani da wasu dandalin Intane don su yaɗa ƙarya game da ƙungiyarmu. Manufarsu ita ce su janye mutane daga bauta wa Jehobah. Mu guji waɗannan dandalin.—Zabura 1:1; 26:4; Romawa 16:17.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba