Sashe 23
Bishara Ta Yaɗu
Bulus ya yi tafiye-tafiye na yin wa’azi a kan ƙasa da teku
BAYAN ya zama mabiyi, Bulus ya yi wa’azin bisharar Mulkin Allah da ƙwazo, kuma hakan ya sa wannan ɗan hamayya a dā ya fuskanci muguwar hamayya. Wannan manzo mai ƙwazo ya tafi wurare masu yawa don ya yi wa’azi, ya yi tafiya zuwa wurare masu nisa don ya yaɗa bishara game da Mulkin da zai cika ainihin manufar Allah ga ’yan Adam.
A lokaci na farko da ya fita yin wa’azi a Listra, Bulus ya warkar da wani mutumi da aka haifa gurgu. Sai mutane suka soma ihu suna cewa Bulus da abokin tafiyarsa Barnaba, alloli ne. Da kyar Bulus da Barnaba suka hana mutanen yin hadayu a gare su. Domin maƙiyan Bulus sun rinjaye su, sai waɗannan mutanen suka yi ta jifan Bulus da dutse har sa’ad da suka ɗauka cewa ya mutu. Bulus ya tsira daga wannan harin kuma bayan haka ya koma birnin don ya ƙarfafa almajiran da kalamai masu ƙarfafawa.
Wasu Yahudawa Kiristoci suna gardama cewa masu bi da ba Yahudawa ba suna bukatan su bi wasu ɓangarorin Dokar Musa. Bulus ya kai batun ga manzanni da dattawan da ke Urushalima. Bayan sun bincika Nassosi dalla-dalla da kuma ja-gorancin ruhu mai tsarki na Allah, waɗannan mutanen suka rubuta wasiƙa ga ikilisiyoyi kuma suka gargaɗe su su guji bautar gumaka, cin jini da dabbar da ba a yanka ba, da kuma zina. Waɗannan dokokin “wajibai” ne, amma bin su ba ya bukatan bin Dokar Musa.—Ayyukan Manzanni 15:28, 29.
A tafiyarsa ta biyu na yin wa’azi, Bulus ya ziyarci Biriya, wato, Helas na zamani. Yahudawan da ke wurin sun karɓi saƙon da hannu biyu-biyu, suna bincika Nassosi a kullum don su tabbatar da koyarwarsa. A nan kuma, hamayya ta tilasta masa ya tafi Atina. A gaban ’yan Atina masu ilimi sosai, Bulus ya ba da jawabi mai ƙarfi wanda misali ne mai kyau na amfani da basira, fahimi, da fasahar magana.
Bayan tafiya na uku na yin wa’azi, Bulus ya tafi Urushalima. Sa’ad da ya ziyarci haikalin da ke wurin, sai wasu Yahudawa suka ta da hargitsi, suna son su kashe shi. Sojojin Roma suka shiga tsakaninsu kuma suka yi wa Bulus tambayoyi. A matsayin ɗan ƙasar Roma, ya kāre kansa a gaban Gwamna Filikus ɗan Roma. Yahudawan sun kasa gabatar da wata shaida a kan tuhumar da suke yi wa Bulus. Don ya hana Fastos, wanda wani gwamna ne ɗan ƙasar Roma, ya miƙa shi ga Yahudawa, sai Bulus ya ce: “Na ɗaukaka roƙo zuwa wurin Kaisar.” Sai Fastos ya ce: “Wurin Kaisar za ka tafi.”—Ayyukan Manzanni 25:11, 12.
Daga nan sai aka ɗauki Bulus a cikin jirgin ruwa zuwa ƙasar Italiya don ya fuskanci shari’a. Domin jirgin ruwan ya yi haɗari, hakan ya sa lokacin ɗari ya same shi a tsibirin Malita. Sa’ad da ya isa ƙasar Roma, ya yi shekara biyu a gidan haya. Ko da yake sojoji suna gadinsa, wannan manzo mai ƙwazo ya ci gaba da yin wa’azin Mulkin Allah ga dukan waɗanda suka ziyarce shi.
—An ɗauko daga Ayyukan Manzanni 11:22–28:31.
◼ Menene ya faru bayan da Bulus ya warkar da wani gurgu a Listira?
◼ Ta yaya aka daidaita tambayar da aka yi game da bin Dokar Musa?
◼ Ta yaya ne Bulus ya sami kansa a Roma, kuma menene ya yi sa’ad da yake wurin?
[Taswira a shafi na 26]
Farawa
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
1 Sama’ila
2 Sama’ila
1 Sarakuna
2 Sarakuna
1 Labarbaru
2 Labarbaru
Ezra
Nehemiya
Esther
Ayuba
Zabura
Misalai
Mai-Wa’azi
Waƙar Waƙoƙi
Ishaya
Irmiya
Makoki
Ezekiel
Daniyel
Hosiya
Joel
Amos
Obadiya
Yunana
Mikah
Nahum
Habakkuk
Zafaniya
Haggai
Zakariya
Malakai
Matta
Markus
Luka
Yohanna
● Ayyukan Manzanni
Romawa
1 Korintiyawa
2 Korintiyawa
Galatiyawa
Afisawa
Filibiyawa
Kolosiyawa
1 Tasalonikawa
2 Tasalonikawa
1 Timotawus
2 Timotawus