B1
Saƙon da Ke Cikin Littafi Mai Tsarki
Jehobah yana da ikon yin sarauta. Yadda yake yin sarauta ne ya fi dacewa. Nufinsa ga duniya da kuma ꞌyanꞌadam zai cika.
Bayan 4026 K.H.Y. “Macijin” ya ƙalubalanci ikon da Jehobah yake da shi na yin sarauta da kuma yadda yake yin sarauta. Jehobah ya yi alkawari zai ta da wata ‘zuriya’ wadda a ƙarshe za ta hallaka macijin, wato Shaiɗan. (Farawa 3:1-5, 15) Amma, Jehobah ya bar ꞌyanꞌadam su yi sarauta da kansu a ƙarƙashin ikon macijin. |
1943 K.H.Y. Jehobah ya gaya wa Ibrahim cewa ‘zuriyar’ da aka yi alkawarin ta za ta fito ta iyalinsa.—Farawa 22:18. |
Bayan 1070 K.H.Y. Jehobah ya tabbatar wa Sarki Dauda da kuma ɗansa Sulemanu daga baya cewa ‘zuriyar’ da aka yi alkawarin ta za ta fito ta iyalinsu.—2 Samaꞌila 7: 12, 16; 1 Sarakuna 9:3-5; Ishaya 9:6, 7. |
29 B.H.Y. Jehobah ya bayyana cewa Yesu ne ‘zuriyar’ da aka yi alkawarin ta, wanda zai gāji kujerar mulkin Dauda.—Galatiyawa 3:16; Luka 1:31-33; 3:21, 22. |
33 B.H.Y. Macijin, wato Shaiɗan ya sari diddigen wannan ‘zuriyar’ ta wajen sa a kashe Yesu. Jehobah ya ta da Yesu zuwa sama kuma ya karɓi amfanin kamiltaccen rai na Yesu. Ta hakan, Allah ya buɗe hanyar gafarar zunubai da kuma ba ꞌyanꞌadam begen rayuwa har abada.—Farawa 3:15; Ayyukan Manzanni 2:32-36; 1 Korintiyawa 15:21, 22. |
Wajen 1914 B.H.Y. Yesu ya jefa Shaiɗan zuwa duniya, kuma Shaiɗan zai kasance a wurin na ɗan lokaci.—Ruꞌuya ta Yohanna 12:7-9, 12. |
Nan gaba Yesu zai ɗaure Shaiɗan na tsawon shekaru dubu ɗaya, saꞌan nan zai murƙushe kansa a alamance, wato zai hallaka shi gabaki-ɗaya. Ainihin nufin Jehobah ga duniya da kuma ꞌyanꞌadam zai cika, za a tsarkake sunansa, kuma za a nuna cewa yadda yake sarauta ne ya fi dacewa.—Ruꞌuya ta Yohanna 20:1-3, 10; 21:3, 4. |