Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • nwt pp. 464-467
  • A1 Ƙaꞌidodin Fassara Littafi Mai Tsarki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • A1 Ƙaꞌidodin Fassara Littafi Mai Tsarki
  • Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah, Allah Ne Mai Ma’amala da Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Fassarar Littafi Mai Tsarki Mai Saukin Fahimta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
A1 Ƙaꞌidodin Fassara Littafi Mai Tsarki

A1

Ƙaꞌidodin Fassara Littafi Mai Tsarki

Asali, an rubuta Littafi Mai Tsarki a Ibrananci, da yaren Aramaik, da yaren Girka na dā. A yau, an fassara cikakkensa ko sashensa zuwa sama da yaruka dubu uku. Yawancin mutane da suke karanta Littafi Mai Tsarki ba su iya asalin yarukan da aka rubuta Littafi Mai Tsarki da su ba. Saboda haka, ya zama dole su yi amfani da wanda aka fassara. Waɗanne ƙaꞌidodi ne ya kamata a bi wajen fassara Littafi Mai Tsarki? Ta yaya aka bi ƙaꞌidodin nan wajen fassara Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya?

Wasu sun ɗauka cewa idan aka fassara Littafi Mai Tsarki kalma bayan kalma, hakan zai taimaka wa mai karatu ya ga cewa maꞌanar ta yi kusa da Littafi Mai Tsarki da aka rubuta da yaruka na asali. Amma ba haka yake a kowane lokaci ba. Ga wasu dalilai:

  • Babu yaruka biyu waɗanda suke da nahawu, da kalmomi, da kuma tsarin rubutu iri ɗaya. Wani farfesa na Ibrananci mai suna S. R. Driver, ya rubuta cewa “bambanci da ke tsakanin yaruka ba kawai nahawu da kuma tushen kalmominsu ba ne, amma har da yadda ake harhaɗa bayanai su zama jimla.” Yadda mutane suke tunani a wannan yare ya yi dabam da yadda mutane suke tunani a wancan yaren. Farfesa Driver ya ci-gaba da cewa: “Saboda haka, tsarin da yaruka suke bi su rubuta jimla ba ɗaya ba ne.”

  • A yau, ba yaren da yake da nahawu da kalmomi da suka yi daidai da na Ibrananci, ko yaren Aramaik, ko yaren Girka da aka rubuta Littafi Mai Tsarki da su. Saboda haka, fassara Littafi Mai Tsarki kalma bayan kalma zai yi wuyar fahimta, a wasu lokuta ma zai iya ba da wata maꞌana dabam.

  • Maꞌanar wata kalmar ko furuci za ta iya canja bisa ga abin da ake magana a kai.

Mafassari zai iya fassara wasu kalmomi daidai yadda suke a yaruka na asali, amma dole ne ya yi hankali sosai yayin da yake hakan.

Ga wasu misalai na yadda fassara kalma bayan kalma yake ba da maꞌana da ba daidai ba:

  • A cikin Nassosi, an yi amfani da kalmomin nan “barci” da kuma “yi barci” saꞌad da ake maganar barci na zahiri ko kuma mutuwa. (Matiyu 28:13; Ayyukan Manzanni 7:60, ƙarin bayani) Idan aka yi amfani da kalmomin nan saꞌad da ake maganar mutuwa, mafassaran Littafi Mai Tsarki sukan yi amfani da “mutu” ko “yi barci cikin mutuwa.” Hakan zai taimaka wa mai karatu kada ya rikice.—1 Korintiyawa 7:39; 1 Tasalonikawa 4:13; 2 Bitrus 3:4.

  • A Afisawa 4:14, manzo Bulus ya yi amfani da wani furuci wanda idan aka fassara shi a zahiri zai zama “yadda mutane suke jefa ɗan lido.” Wannan karin magana na zamanin dā yana nuni ne ga yadda wasu suke cucin mutane saꞌad da suke amfani da ɗan lido. A yawancin yaruka, idan aka fassara wannan furucin a zahiri, ba zai ba da maꞌana ba. Yadda aka fassara furucin nan zuwa “amfani da wayo” ya fi sauƙin fahimta.

  • A Romawa 12:11, an yi amfani da wani furucin yaren Girka wanda a zahiri yake nufin “ruhu da yake tafasa.” Maꞌanar furucin nan a Hausa ba ɗaya ba ne da yadda yake a yaren Girka. Don haka, an fassara shi zuwa “ruhu mai tsarki ya sa ku himma” a wannan juyin.

  • Wani layin rubutu cikin Littafi Mai Tsarki na asali da aka yi amfani da shi wajen fassara

    MATIYU 5:3

    Fassara a zahiri: “masu talauci a ruhu”

    Maꞌana: “waɗanda suka san cewa suna bukatar ja-gorancin Allah”

    Saꞌad da Yesu yake Huɗuba a kan Dutse, ya yi amfani da furuci da ake yawan fassara zuwa “masu albarka ne masu talauci a ruhu.” (Matiyu 5:3, King James Version) Amma a yaruka da yawa, idan aka fassara wannan a zahiri, ba za a gane abin da ake faɗa ba. A wasu yaruka, idan aka fassara wannan furucin a zahiri, yana iya nufin cewa “masu talauci a ruhu” suna da taɓin hankali ko ba su da ƙarfi da kuma niyyar yin wani abu. Amma a nan, Yesu yana koya wa mutane cewa za su yi farin ciki idan sun fahimci cewa suna bukatar ja-gorancin Allah ne, ba a kan yadda za su biya bukatunsu na zahiri ba. (Luka 6:20) Saboda haka, fassara furucin nan zuwa “waɗanda suka san cewa suna bukatar ja-gorancin Allah” ko kuma “waɗanda suka san cewa suna bukatar Allah” ya fito da maꞌanar da ta yi daidai da furucin a yaren Girka.—Matiyu 5:3; juyin The New Testament in Modern English.

  • A wurare da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar Ibrananci da aka fassara zuwa “kishi” ta yi daidai da na Hausa, wato mutum ya yi fushi don amininsa ya ci amanarsa ko kuma yin hassada don dukiyoyin wasu. (Karin Magana 6:34; Ishaya 11:13) Amma kalmar nan a Ibrananci tana kuma iya nufin abu mai kyau. Alal misali, ana iya amfani da ita wajen nuna irin “himmar” da Yesu da wasu amintattun bayin Allah suke da ita ga Allah da kuma bautarsa.—Yohanna 2:17; 2 Korintiyawa 9:2.

  • A wurare da yawa, kalmar yaren Girka da aka fassara zuwa ‘fuska’ a Matiyu 6:17, tana da maꞌana dabam-dabam. Bisa ga abin da ake magana a kai, ana iya fassara kalmar zuwa ‘yanayi,’ ko ‘halaye,’ ko kuma a wata hanya dabam.—Matiyu 16:3; Yahuda 16, ƙarin bayani.

    Ana yawan fassara kalmar nan prosopon a yaren Girka zuwa ‘fuska,’ amma bisa ga abin da ake magana a kai, ana iya fassara kalmar zuwa ‘yanayi,’ ko kuma ‘halaye.’

Saboda waɗannan dalilan, idan ana fassara Littafi Mai Tsarki ba kawai ana canja wata kalma a yare na asali zuwa kalmar da ke kama da ita a wani yare a duk wurin da ta bayyana ba ne. Mafassarin zai yi amfani da basira don ya zaɓi kalmar da ta dace a yarensa da ta fi ba da maꞌanar abin da aka faɗa a yare na asali. Ƙari ga haka, zai bukaci ya yi fassarar a hanyar da za ta yi daidai da nahawu da kuma tsarin rubutu na yarensa, ta hakan fassarar za ta yi sauƙin karantawa.

A wani ɓangare kuma, dole ne a guji yawan canja kalmomin. Mafassari da ke yawan amfani da wasu kalmomi dabam saꞌad da yake fassara Littafi Mai Tsaki bisa ga yadda ya fahimci abin da ake magana a kai, zai iya ɓatar da maꞌanar abin da aka faɗa a yare na asali. Ta yaya? Cikin kuskure mafassarin zai iya shigar da raꞌayinsa cikin abin da ya fassara da nufin cewa abin da ake nufi a yare na asali ke nan ko kuma ya cire muhimman bayanai da suke cikin yare na asali. Saboda haka, ko da yake canja kalmomi da aka yi amfani da su a yare na asali zai iya sa fassarar ta yi sauƙin karantawa, hakan zai iya hana mai karatu fahimtar ainihin abin da ake nufi.

Abin da mafassari ya yi imani da shi zai iya shafan yadda ya yi fassara. Alal misali, Matiyu 7:13 ta ce: “Ƙofar zuwa hallaka na da girma kuma hanyarta na da fāɗi.” Wataƙila abin da wasu mafassara suka yi imani da shi ne ya sa suka fassara shi zuwa “gidan wuta” maimakon yin amfani da abin da kalmar a yaren Girka take nufi, wato “hallaka.”

Ƙari ga haka, dole ne mafassarin Littafi Mai Tsarki ya tuna cewa an rubuta Littafi Mai Tsarki da kalmomin da mutane suke amfani da su yau da kullum, har da manoma, da makiyaya, da kuma masu kamun kifi. (Nehemiya 8:8, 12; Ayyukan Manzanni 4:13) Saboda haka, idan aka fassara Littafi Mai Tsarki da kyau, hakan zai sa mutane da suke marmarin koyon gaskiya su fahimce shi, ko daga ina ne suka fito. An fi so a yi amfani da kalmomin da mutane suke amfani da su yau da kullum fiye da waɗanda ba a yawan amfani da su.

Mafassara da yawa sun yi abin da bai kamata su yi ba saꞌad da suka cire sunan Allah, wato Jehobah daga juyin Littafi Mai Tsarki na zamaninmu, duk da cewa akwai sunan a cikin rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na dā. (Ka duba Wasu Bayanai na 04.) A juyin Littafi Mai Tsarki da yawa, an canja sunan da laƙabi kamar “Ubangiji,” kuma wasu daga cikinsu sun sa ya yi kamar Allah bai da suna. Alal misali, ga yadda aka fassara adduꞌar Yesu da ke Yohanna 17:26 a wasu juyin Littafi Mai Tsarki: “Na sa su san ka,” Yohanna 17:6 kuma: “Na bayyana ka ga waɗanda ka ba ni.” Amma ga yadda ya kamata a fassara adduꞌar Yesu: “Na sa su san sunanka,” da kuma “Na sa mutanen da ka ba ni daga duniyar nan su san sunanka.”

A Fassarar Sabuwar Duniya ta farko da aka yi da Turanci, an faɗa a gabatarwar cewa: “Ba ma yawan canja kalmomin da aka yi amfani da su a yare na asali. Mun yi iya ƙoƙarinmu mu yi fassarar daidai yadda yake a yare na asali a duk inda karin maganar Turanci na zamani zai bar mu mu yi hakan, da inda yin fassara daidai yadda yake a yare na asali ba zai canja maꞌanar ba.” Don haka, Kwamitin Juyin Fassarar Sabuwar Duniya ya yanke shawarar cewa idan zai yiwu, zai yi amfani da kalma ko kuma furuci da ya yi daidai da waɗanda aka yi amfani da su a yare na asali, kuma ya guji yin amfani da kalmomin da za su sa fassarar ta yi wuyar karantawa ko kuma ta canja maꞌanar. A sakamakon haka, mutane za su iya karanta Littafi Mai Tsarki cikin sauƙi, kuma mai karatu zai kasance da cikakkiyar tabbaci cewa an fassara saƙon Allah daidai yadda ya kamata.—1 Tasalonikawa 2:13.

Dole ne fassarar Littafi Mai Tsarki mai kyau ya:

  • Tsarkake sunan Allah ta wajen maido da sunan a inda ya kamata ya kasance a cikin Nassosi.—Matiyu 6:9.

  • Faɗa ainihin abin da Allah ya sa a rubuta ta wurin ruhu mai tsarki.—2 Timoti 3:16.

  • Fassara furuci daga yare na asali a zahiri zuwa yare na biyun, idan zai yi daidai da kalmomi da kuma yadda ake rubutu a yare na biyun.

  • Fassara ainihin maꞌanar kalmar ko kuma furucin, idan fassara kalmar ko furucin a zahiri zai canja maꞌanar.

  • Yi amfani da kalmomi da kuma furuci masu sauƙin ganewa da kuma sauƙin karantawa.—Nehemiya 8:8, 12.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba