Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Satumba p. 32
  • Yesu “Ya Koyi Yin Biyayya”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yesu “Ya Koyi Yin Biyayya”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Makamantan Littattafai
  • Biyayya—Muhimmin Darasi ne na Yarantaka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Jehobah Yana Son Ka Yi Masa Biyayya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • “’Ya’ya, Ku Yi Biyayya Da Waɗanda Suka Haife Ku”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ka Koyi Biyayya Yayin Da Ƙarshe Ya Matso Kusa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Satumba p. 32

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE NUFI

Yesu “Ya Koyi Yin Biyayya”

Yesu ya yi shekaru aru-aru yana yi wa Jehobah biyayya. (Yoh. 8:29) To, me ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya koyi yin biyayya ta hanyar azabar da ya sha”?—Ibran. 5:8.

Saꞌad da Yesu yake duniya, ya fuskanci yanayoyin da babu irinsu a sama. Alal misali, iyayensa suna ƙaunar Jehobah amma su ajizai ne. (Luk. 2:51) Ya sha wahala a hannun mugayen shugabannin addinai da kuma masu mulki. (Mat. 26:59; Mar. 15:15) Ƙari ga haka, an azabtar da shi kafin ya mutu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya ƙasƙantar da kansa ta wurin yin biyayya, biyayyar da ta kai shi har ga mutuwa.”—Filib. 2:8.

Waɗannan abubuwan sun sa Yesu ya koyi yin biyayya a hanyar da bai taɓa yi ba a sama. Hakan ya sa ya zama wanda ya dace ya zama Sarki da kuma Babban Firist domin ya fahimci yanayinmu da kyau. (Ibran. 4:15; 5:9) Bayan Yesu ya koyi biyayya daga azabar da ya sha, Jehobah ya ƙara daraja shi, kuma ya yi amfani da shi a hanyoyi da dama. Mu ma Jehobah zai ƙara daraja mu idan mun ci-gaba da yin biyayya ko da muna shan wuya.—Yak. 1:4.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba