Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Satumba pp. 26-30
  • Jehobah Ya Taimaka Mana Mu Ci-gaba da Yin Farin Ciki a Duk Inda Muka Samu Kanmu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Ya Taimaka Mana Mu Ci-gaba da Yin Farin Ciki a Duk Inda Muka Samu Kanmu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah Ya Albarkace Ni Fiye da Yadda Na Yi Tsammani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Jehobah Ya ‘Daidaita Hanyoyina’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Yadda Za Mu Yi Farin Ciki Sa’ad da Muka Soma Sabuwar Hidima
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Mun Koyi Darussa da Dama Daga Malamin da Babu Kamar Sa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Satumba pp. 26-30
Mats da Ann-Catrin suna tsaye kusa da motarsu a wani ƙauye.

TARIHI

Jehobah Ya Taimaka Mana Mu Ci-gaba da Yin Farin Ciki a Duk Inda Muka Samu Kanmu

MATS DA ANN-CATRIN KASSHOLM NE SUKA BA DA LABARIN

YIN farin ciki a duk inda ka samu kanka ba abu ne mai sauƙi ba. Amma wasu maꞌaurata ꞌyan Sweden sun yi hakan duk da cewa sun ga kansu a wurare dabam-dabam. Bari mu ga abin da ya taimaka musu.

Ɗanꞌuwa da ꞌYarꞌuwa Kassholm sun halarci Makarantar Gilead a 1979, kuma sun yi shekaru suna hidima a wurare da dama, kamar Iran, da Maurishiyas, da Miyamma, da Tanzaniya, da Yuganda, da kuma Zaire. Wani malaminsu a Makarantar Gilead mai suna Jack Redford, ya faɗi wani abin da ya taimaka musu a duk lokacin da aka canja musu wurin da suke hidima, kuma hakan ya faru sau da yawa. Bari su bayyana mana abin da ya faru.

Don Allah, ku gaya mana yadda kuka samu gaskiya.

Mats ya ce: Mahaifina yana zama a ƙasar Poland ne a lokacin da aka yi Yaƙin Duniya na 2, kuma ya ga munafuncin da aka yi ta yi a Cocin Katolika. A yawancin lokuta yakan ce, “Na san cewa akwai addini na gaskiya a wani wuri!” Daga baya, na gano cewa abin da ya faɗa gaskiya ne. Na sayi littattafai da yawa da aka yi gwanjon su. Ɗaya daga cikin littattafan da na saya shi ne, Gaskiya Mai-bishe Zuwa Rai Madawwami. Jigon littafin ya burge ni sosai, kuma na karanta littafin gabaki ɗaya a daren da na saye shi. Da na gama karanta shi, sai na gane cewa na samu addini na gaskiya!

Daga watan Afrilu na shekarar 1972, na karanta littattafai da dama na Shaidun Jehobah, kuma na samu amsar tambayoyina. Na ji kamar ɗan kasuwa da ke misalin da Yesu ya bayar. Saꞌad da ya sami wani luꞌuluꞌu mai daraja sosai, ya sayar da komen da yake da shi don ya sayi luꞌuluꞌun. Ni ma na yi watsi da muraɗina na zuwa jamiꞌa don in zama likita, kuma na yanke shawarar bauta wa Jehobah da dukan zuciyata. (Mat. 13:​45, 46) Na yi baftisma a ran 10 ga Disamba, 1972.

A cikin shekara ɗaya, iyayena da ƙanena ma sun yi baftisma. Na soma hidima ta cikkaken lokaci a Yuli 1973. A cikin majagaba masu ƙwazo a ikilisiyarmu, akwai wata kyakkyawa mai ƙaunar Jehobah mai suna Ann-Catrin. Mun soma soyayya kuma muka yi aure 1975. Mun yi shekaru huɗu muna zama a wani gari mai suna Strömsund, wuri ne mai kyau a ƙasar Sweden, kuma mutane a wurin suna jin waꞌazinmu.

Ann-Catrin ta ce: Mahaifina ya koyi gaskiya a lokacin da ya kusan gama jamiꞌa a Stockholm. A lokacin watana uku ne kawai a duniya, duk da haka, mahaifina yakan kai ne taro da kuma waꞌazi. Mahaifiyata ba ta so hakan ba, kuma ta yi ƙoƙarin nuna cewa abin da Shaidun Jehobah suke koyarwa ƙarya ne. Amma ta gagara. Da shigewar lokaci, ita ma ta yi baftisma. Na yi baftisma saꞌad da nake shekara 13, kuma na soma hidimar majagaba a lokacin da nake shekara 16. Bayan na yi hidima a Umeå, wurin da ake bukatar masu shela, sai na zama majagaba na musamman.

Bayan da muka yi aure, mun yi farin cikin taimaka wa mutane da yawa su koyi gaskiya. Ɗaya daga cikinsu ita ce wata matashiya mai suna Maivor, ta daina aikin da zai sa ta yi suna kuma ta sami kuɗi sosai, don ta bauta wa Jehobah. Ita da ƙanwata sun yi hidimar majagaba tare. Sun halarci Makarantar Gilead a 1984, kuma suna hidima a matsayin masu waꞌazi a ƙasashen waje a ƙasar Ecuador.

Me ya taimaka muku ku ci-gaba da yin farin ciki a hidimarku?

Mats ya ce: An yi ta canja mana wuraren da za mu yi hidima. Amma wani abin da ya taimaka mana shi ne, yin iya ƙoƙarinmu don mu bi misalin Yesu, musamman yadda ya kasance da sauƙi kai. (Kol. 2:​6, 7) Alal misali, maimakon mu ɗauka cewa ꞌyanꞌuwan da muke tare da su za su riƙa yin abubuwa yadda muke so, muna ƙoƙari mu san dalilin da ya sa suke yin abubuwa yadda suke yi. Muna ƙoƙari mu gane yadda suke tunani da kuma alꞌadunsu. Yin koyi da Yesu ya sa ya yi mana sauƙi mu shaƙu da ꞌyanꞌuwan, kuma mu ci-gaba da farin ciki a hidimarmu.—Zab. 1:​2, 3.

Mats da Ann-Catrin ɗauke da akwatinsu da kuma kayan abinci.

Yin tafiye-tafiye ya zama musu jiki don sun saba ziyartar ikilisiyoyi

Ann-Catrin ta ce: Itacen da aka dasa tana bukatar hasken rana don ta yi girma da kyau. Kamar itacen, Jehobah ne hasken ranarmu. (Zab. 84:11) Jehobah ya ba mu ꞌyanꞌuwa maza da mata masu ƙauna. Alal misali, a Tehran, a ƙasar Iran, ꞌyanꞌuwanmu suna bayarwa hannu sake, kuma suna karɓan baƙi hannu bibbiyu. Hakan na tuna mana da wasu mutanen da aka ambata a Littafi Mai Tsarki da suke da irin halin nan. Da za mu so mu zauna a Iran, amma a Yuli 1980, an sa wa aikinmu takunkumi a ƙasar kuma aka ce mu bar ƙasar cikin kwana biyu. Hakan ya sa aka tura mu Zaire (wurin da ake kiran Kwango yanzu) a Afirka.

Ƙaramin gida a wani ƙauye a Zaire.

Wuraren da muka yi hidima a ƙasar Zaire, a 1982

Saꞌad da na ji cewa an tura mu hidima a Afirka, na fashe da kuka. Labaran da na ji game da macizai da cututtuka a Afirka sun sa na ji tsoro sosai. Amma wani ɗanꞌuwa da matarsa da suka yi shekaru da yawa suna hidima a Afirka sun gaya mana cewa: “Ai ba ku taɓa zuwa wurin ba! Kada ku ji tsoro, mun san cewa in kun je za ku so zama a wurin.” Abin da suka faɗa gaskiya ne! ꞌYanꞌuwa a wurin suna da kirki kuma suna nuna ƙauna. Bayan shekara shida an sa wa aikinmu takunkumi a wurin, sai aka ce mu bar ƙasar. A lokacin, na yi murmushi don raꞌayina ya canja kwata-kwata game da Afirka. Har ma ina ta alla-alla a bar mu a Afirka.

Waɗanne albarku ne kuka samu a hidimarku?

Ann-Catrin tana zaune a kan kujera kusa da motarsu da suke kwana a ciki.

Ɗakinmu ke nan a Tanzaniya, a 1988

Mats ya ce: Hidimarmu ta sa mun ƙulla abota da ꞌyanꞌuwa masu waꞌazi a ƙasashen waje da suka fito daga wurare dabam-dabam. Ƙari ga haka, a wasu wuraren da muka yi hidima, mun yi farin ciki sosai don mun sami ɗalibai da yawa da muke nazari da su. A wasu lokuta, nakan yi nazari da wajen mutane 20, matata ma hakan! Ba zan taɓa manta da irin ƙaunar da ꞌyanꞌuwan da ke Afirka suka nuna mana ba. Saꞌad da muke kai wa ikilisiyoyi ziyara a Tanzaniya, mukan kwana a cikin motarmu, kuma ꞌyanꞌuwan suna tabbata cewa mun samu abin da muke bukata duk da cewa su talakawa ne sosai. (2 Kor. 8:3) Wani abin da muke jin daɗin sa sosai shi ne lokacin da muke labarai. Ni da matata mukan yi hakan da dare. Mukan tattauna abubuwan da suka faru a ranar, kuma mu gode wa Jehobah don yadda ya taimaka mana.

Ann-Catrin ta ce: Ina farin ciki sosai da na sami damar sanin ꞌyanꞌuwa maza da mata daga wurare dabam-dabam a faɗin duniya. Mun koyi sabbin yaruka kamar su Farsi, da Faransanci, da Luganda, da kuma Swahili, kuma mun koyi alꞌadu dabam-dabam. Mun taimaka wa waɗanda ba su daɗe da yin baftisma ba su ƙarfafa bangaskiyarsu, mun sami abokan kirki, kuma mun ji daɗin bauta wa Jehobah tare da su.—Zaf. 3:9.

Mun kuma ga halittun Jehobah dabam-dabam masu kyau sosai. A duk lokacin da aka canja mana inda za mu yi hidima, muna ji kamar Jehobah yana tare da mu yana nuna mana hanya. Ya koya mana abubuwan da ba za mu iya sani ba da kanmu.

Hotuna: Na 1. Mats da Ann-Catrin suna yi wa wata mata da yaranta waꞌazi. Na 2. Ann-Catrin tana yi wa wata mata ꞌyar Maasai waꞌazi.

Waꞌazi a wurare dabam-dabam a Tanzaniya

Waɗanne matsaloli ne kuka fuskanta kuma me ya taimaka muku ku jimre?

Mats ya ce: A wasu lokuta mun kamu da cututtuka kamar su, maleriya, wato zazzabin cizon sauro. Sau da sau, an yi wa Ann-Catrin tiyata ba zato. Mun kuma damu don iyayenmu da suka tsufa. Mun gode wa ƙannenmu don su ne suka yi ta kula da su. Kuma sun yi hakan da haƙuri da farin ciki da kuma ƙauna. (1 Tim. 5:4) Ko da yake muna da nisa da su, mun yi abin da za mu iya yi don mu taimaka. Amma a wasu lokuta muna baƙin ciki don muna ganin ya kamata mu yi abin da ya fi abin da muka yi.

Ann-Catrin ta ce: A 1983, lokacin da muke hidima a Zaire, na yi fama da ciwon amai da gudawa, wato kwalera mai tsanani. Har likita ya gaya wa Mats cewa, “Ka fitar da ita ƙasar waje yau ɗin nan.” Washegari mun kama hanya zuwa Sweden a cikin wani jirgin sama mai kwasan kaya.

Mats ya ce: Mun yi ta kuka don mun ga kamar ba za mu ƙara dawowa yin hidima a ƙasar waje ba. Ko da yake likitan ya ga kamar Ann-Catrin ba za ta sami sauƙi ba, daga baya ta sami sauƙi. Bayan shekara ɗaya, sai muka koma Zaire, kuma muka soma hidima a wata ƙaramar ikilisiya da ke Lubumbashi da ake yaren Swahili.

Ann-Catrin ta ce: A lokacin da muke Lubumbashi, na yi ɓari. Ko da yake ba mu da niyyar haifan yara, yadda cikin ya zube, ya sa ni baƙin ciki sosai. A lokacin, Jehobah ya ba mu wani abu mai daraja da ba mu yi tsammani ba. Mun fara yin nazari da mutane da yawa fiye da yadda muka taɓa yi a dā. Kafin shekara ɗaya, adadin masu shela ya tashi daga 35 zuwa 70, adadin masu halartan taro kuma ya tashi daga 40 zuwa 220. Mun mai da hankali a kan yin waꞌazi kuma albarkar da Jehobah ya yi mana, ya taꞌazantar da ni. Har ila, mukan yi tunani kuma mu yi magana game da ɗanmu. Muna marmarin lokacin da Jehobah zai sa mu daina baƙin ciki kwata-kwata a aljanna.

Mats ya ce: Daga baya, Ann-Catrin ta yi fama da yawan gajiya da nauyin jiki sosai. A lokacin, an gano cewa ni ma ina fama da kansar hanji kuma ana bukatar a yi min tiyata. Amma yanzu na sami lafiya, kuma matata tana iya ƙoƙarinta a bautarta ga Jehobah.

Mun san cewa ba mu kaɗai ba ne muke fama da matsaloli. Bayan kisan ƙare dangi da aka yi a ƙasar Ruwanda a 1994, mun ziyarci abokanmu da yawa da suke zama a sansanin ꞌyan gudun hijira. Ganin yadda suka riƙe bangaskiyarsu da jimirinsu, da kuma yadda suke bayarwa hannu sake duk da yanayi mai wuya da suke ciki, ya koya mana cewa Jehobah yana da ikon kiyaye mutanensa, a lokacin da suke cikin wahala.—Zab. 55:22.

Ann-Catrin ta ce: Mun fuskanci wata matsala kuma, a lokacin da muka halarci taron keɓe reshen ofishi na Yuganda, da aka yi a 2007. Bayan taron, mun kama hanyar komawa Nairobi, da ke ƙasar Kenya, tare da wasu ꞌyanꞌuwa wajen 25 da suke hidima a matsayin masu waꞌazi na ƙasashen waje, da kuma hidima a Bethel. Kafin mu shiga ƙasar Kenya, sai kwatsam, wata babbar mota da ke zuwa a ɗayan gefen ta zo ta shiga gefenmu, sai muka yi karo da juna. Direbanmu da wasu ꞌyanꞌuwanmu biyar sun mutu nan take. Wata ꞌyarꞌuwa ma ta mutu daga baya a asibiti. Muna marmarin ganin lokacin da za mu sake ganin abokanmu!—Ayu. 14:​13-15.

Da shigewar lokaci, raunukan da na ji sun warke. Amma ni da maigidana da wasu ꞌyanꞌuwa muna cikin waɗanda suka ci-gaba da fama da ciwon tsananin damuwa don wannan abin da ya faru. Nawa ciwon yakan tā da ni da dare, nakan ji kamar zuciyata za ta fashe. Hakan yakan ba ni tsoro sosai. Amma yin adduꞌa ga Jehobah, da karanta da kuma yin tunani a kan nassosin da muke so, sun taimaka mana sosai. Ƙari ga hakan, mun nemi taimakon likitocin da suka ƙware, kuma hakan ya taimaka mana. A yanzu dai, mun sami sauƙi sosai. Kuma muna roƙon Jehobah ya taimaka mana mu ƙarfafa ꞌyanꞌuwan da suke fama da irin wannan cutar.

Saꞌad da kuke ambata abubuwan da suka taimaka muku ku jimre, kun gaya mana cewa Jehobah ya riƙe ku kamar “ɗanyen kwai.” Mene ne hakan yake nufi?

Mats ya ce: Masu yin yaren Swahili ne suke wannan ƙarin maganar, sukan ce, “An ɗauke mu kamar ɗanyen kwai.” Kamar yadda mutum yakan riƙe ɗanyen kwai da kyau don kar ya fashe, haka ma Jehobah ya riƙe mu kuma ya taimaka mana a duk hidimar da muka yi. A kowane lokaci, muna samun abin da muke bukata, har ma fiye da abin da muke bukata. Wata hanya da muka ga ƙauna da kuma taimakon Jehobah ita ce, ta wajen tausayin da Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta nuna mana.

Ann-Catrin ta ce: Zan so in ambata wani labari da ya nuna yadda Jehobah ya taimaka mana. Wata rana, an kira ni a waya, kuma an gaya min cewa babana a Sweden, yana rashin lafiya sosai kuma yana asibiti. A lokacin, maigidana yana kan samun sauƙi daga cutar zazzabin cizon sauro. Kuma ba mu da kuɗin shiga jirgin sama da zai kai mu gida. Sai muka yanke shawara cewa za mu sayar da motarmu. Ana nan, sai wayarmu ta sake bugawa sau biyu. Na farko, wasu maꞌaurata ne suka kira, sun ji cewa babana bai da lafiya kuma sun ce za su biya wa ɗayanmu kuɗin jirgi. Na biyun kuma, wata ꞌyarꞌuwa da ta tsufa ce ta kira, ta ce akwai kuɗin da ta ajiye a cikin asusunta. Kuma a kan asusun ta rubuta cewa, “Na wanda yake cikin bukata.” A cikin ꞌyan mintoci, Jehobah ya taimaka mana mu iya biyan kuɗin jirgi!—Ibran. 13:6.

Me kuka koya daga fiye da shekaru 50 da kuka yi kuna hidima ta cikakken lokaci?

Mats da Ann-Catrin suna tsaye kusa da juna suna dariya.

A inda muke hidima yanzu a Miyamma

Ann-Catrin ta ce: Na koyi cewa za mu sami ƙarfin jimrewa ta wajen kasancewa da “kwanciyar hankali da dogara” ga Jehobah. Idan muka dogara ga Jehobah zai yi yaƙi a madadin mu. (Isha. 30:15; 2 Tar. 20:​15, 17) Da yake mun yi iya ƙoƙarinmu a kowace hidima da aka ba mu, mun sami albarku da yawa, fiye da yadda za mu samu da a ce wani abu muka yi da rayuwarmu.

Mats ya ce: Abu mafi muhimmanci da na koya shi ne dogara ga Jehobah a kowane yanayin da nake ciki, kuma in ga abin da zai yi a madadi na. (Zab. 37:5) Bai taɓa fasa taimaka mini ba kamar yadda ya yi alkawari. Kuma har yanzu muna ganin taimakonsa a hidimar da muke yi a Bethel da ke ƙasar Miyamma.

Fatanmu ita ce ꞌyanꞌuwa matasa da yawa da suke son su faɗaɗa hidimarsu ga Jehobah su ma su more irin ƙauna marar canjawa da Jehobah ya nuna mana. Muna da tabbaci cewa za su yi hakan idan suka bar Jehobah ya ci-gaba da taimaka musu su kasance da farin ciki a duk inda suke hidima.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba