Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb23 Satumba p. 7
  • Dattawan da Suke Ƙoƙari Su Taimaka wa Bayin Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Dattawan da Suke Ƙoƙari Su Taimaka wa Bayin Jehobah
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Makamantan Littattafai
  • Ka ‘Kira Dattawa’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Yadda Za A Nuna wa Mai Zunubi Kauna da Jinkai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • ꞌYanꞌuwa Maza​—⁠Kuna Kokari don Ku Zama Dattawa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Makiyaya, Ku Yi Koyi da Makiyaya Mafi Girma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
mwb23 Satumba p. 7

RAYUWAR KIRISTA

Dattawan da Suke Ƙoƙari Su Taimaka wa Bayin Jehobah

Mutane da yawa ba su da raꞌayi mai kyau game da masu ja-goranci. Dalilin shi ne, tarihi ya nuna cewa mutane da yawa sun yi amfani da ikonsu a hanyar da ba ta dace ba. (Mi 7:3) Muna godiya don an koya wa dattawa yadda za su yi amfani da ikon da aka ba su a cikin ikilisiya wajen taimaka wa bayin Jehobah.—Es 10:3; Mt 20:25, 26.

Dattawa sun bambanta da mutanen da suke da iko a duniya. Dattawa suna yin aikinsu ne domin suna ƙaunar Jehobah da kuma mutanensa. (Yoh 21:16; 1Bi 5:1-3) Da taimakon Yesu, dattawa suna taimaka wa kowane mai shela ya ji daɗin zama tare da bayin Jehobah kuma ya ci gaba da kusantar Jehobah. Suna a shirye su ƙarfafa ꞌyanꞌuwa da kuma taimaka musu idan suna bukatar jinyar gaggawa ko idan balaꞌi ya auku. Idan kana bukatar taimako, kada ka yi jinkirin gaya wa wani dattijo a ikilisiyarku.—Yak 5:14.

Hoto daga bidiyon “Dattawa Suna Kula da Tumakin Allah.” Wani dattijo ya rungumi Elias yayin da suke gai da juna.

KU KALLI BIDIYON NAN DATTAWA SUNA KULA DA TUMAKIN ALLAH, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Ta yaya Mariana ta amfana daga taimakon dattawa?

  • Ta yaya Elias ya amfana daga taimakon dattawa?

  • Yaya abin da ya faru da ꞌyanꞌuwan nan ya sa ka ji game da aikin da dattawa suke yi?

Ka gaya wa dattawa . . .

  • idan ka canja adireshi ko lambar wayarka

  • idan kana fama da wata jarrabawa

  • idan za ka yi tafiya na dogon lokaci

  • idan kana fama da rashin lafiya mai tsanani ko idan an kwantar da kai a asibiti

  • idan ka yi zunubi mai tsanani

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba