Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb23 Maris p. 13
  • Yadda Za a Yi Amfani da Bidiyoyin Nazari

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za a Yi Amfani da Bidiyoyin Nazari
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Makamantan Littattafai
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yin Amfani da Bidiyoyi don Koyarwa
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Yaya Shaidun Jehobah Suke Nazarin Littafi Mai Tsarki da Mutane?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
  • Ka Yi Amfani da Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! don Ka Sa Ɗalibanka Su Kasance da Bangaskiya
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Ka Yi Amfani da Bidiyoyi don Ka Koyar da Dalibanka
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
mwb23 Maris p. 13
Wata ꞌyarꞌuwa tana nuna wa wata mata bidiyon “Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki?​—Cikakken Bidiyon” da naꞌuranta.

RAYUWAR KIRISTA

Yadda Za a Yi Amfani da Bidiyoyin Nazari

Muna da bidiyoyi huɗu da muke amfani da su saꞌad da muke waꞌazi. Me ya sa aka shirya kowannensu?

  • Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki?​—Cikakken Bidiyon, wannan bidiyo ne da aka shirya don a taimaka wa mutane su so Littafi Mai Tsarki ko da wane addinni ne suke bi. Bidiyon ya ƙarfafa mutane su nemi amsoshin tambayoyi game da rayuwa a cikin Littafi Mai Tsarki kuma ya ɗan nuna wasu amsoshi da za a samu a ciki. Ya bayyana yadda mutum zai nemi a riƙa nazarin Littafi Mai Tsarki da shi.

  • Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? (gajeren bidiyon), wannan bidiyon yana kama da cikakken bidiyon, amma tsawonsa kashi uku ne na cikakken bidiyon. Wannan zai fi dacewa da yankunan da mutanen ba su da lokaci.

  • Yaya Ake Gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki? bidiyo ne da aka shirya don a sa mutane su so nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ya amsa wasu tambayoyin da mutane suke yi game da nazari, da kuma yadda mutum zai nemi a riƙa nazarin Littafi Mai Tsarki da shi.

  • Maraba da Zuwa Nazarin Littafi Mai Tsarki, bidiyo ne da aka shirya don a nuna wa ɗalibai. Ko da yake an gabatar da bidiyon a shafi na biyu na littafin Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! za a iya nuna wa ɗalibi saꞌad da aka soma tattauna ƙasidar Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! da shi. Bidiyon ya bayyana abin da ke cikin littafin da abin da ɗalibin zai koya saꞌad da yake nazarin.

Ko da yake an shirya kowane bidiyon don manufa dabam-dabam, za mu iya nuna wa mutane ko kuma mu tura musu kowannensu saꞌad da yin hakan ya dace. Ya kamata masu shela su san bayanai cikin bidiyon da kyau kuma su yi amfani da su sosai a waꞌazi.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba