Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb23 Janairu p. 11
  • Ku Nemi Sanin Raꞌayin Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Nemi Sanin Raꞌayin Allah
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Ka Tsai da Shawarwari da Ke Faranta wa Jehobah Rai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Karatun Littafi Mai Tsarki Kowace Rana da Neman Hikima
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Iyaye, Ku Koya wa Yaranku Yadda Za Su Sa Allah Farin Ciki
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
mwb23 Janairu p. 11
Hoton da aka dauko daga bidiyon “Wajibi Ne Ku Yi Tsere da Jimiri​—Ku Ci Abinci Mai Gina Jiki.” Rebekah tana amfani da kasidar “The Origin of Life​—Five Questions Worth Asking” don ta yi bincike.

RAYUWAR KIRISTA

Ku Nemi Sanin Raꞌayin Allah

Ya kamata mu riƙa faranta ran Jehobah a duk abubuwan da muke yi. (K. Ma 27:11) Don mu yi haka, muna bukata mu tsai da shawarwarin da suka jitu da raꞌayin Allah, ko da babu wata takamaiman dokar da za mu bi. Amma me zai taimaka mana?

Zai dace mu riƙa nazarin Littafi Mai Tsarki. A duk lokacin da muka karanta Littafi Mai Tsarki, kamar muna sauraron Jehobah ne. Za mu iya sanin raꞌayin Jehobah ta wajen lura da yadda ya yi shaꞌani da mutanensa da kuma bincika misalan waɗanda suka yi abin da ya dace da waɗanda ba su yi abin da ya dace ba a gabansa. Idan muna so mu yanke shawara, ruhu mai tsarki zai iya taimaka mana mu tuna da muhimman darussa da ƙaꞌidodin da muka koya daga Kalmar Allah.​—Yoh 14:26.

Ku riƙa bincike. Idan kana so ka yanke shawara, ka tambayi kanka, ‘waɗanne ayoyi ne ko labarai a Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka mini in san raꞌayin Jehobah a kan wannan batun?’ Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka kuma ka yi amfani da kayan binciken da ke yarenku don ka sami ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka maka a yanayinka, kuma ka yi amfani da su.​—Za 25:4.

KU KALLI BIDIYON NAN WAJIBI NE KU YI TSERE DA JIMIRI​—KU CI ABINCI MAI GINA JIKI, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Waɗanne matsaloli ne matashiyar da aka nuna a bidiyon ta fuskanta?

  • Ta yaya za ka yi amfani da kayan bincike saꞌad da ka fuskanci irin matsalolin nan?

  • Ta yaya za mu amfana idan muka yi bincike kuma muka yi nazarin da zai taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau?​—Ibr 5:​13, 14

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba