Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb23 Janairu p. 7
  • Ku Yi Shiri Yanzu Don Jinyar Gaggawa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Yi Shiri Yanzu Don Jinyar Gaggawa
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Makamantan Littattafai
  • Kana Jinkirin Cika Ta Kuwa?
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Kun San Zaɓin da Kuke da Shi?
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Ka Yi Shiri don Jinyar Gaggawa?
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Ra’ayin Allah Game da Jini
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
mwb23 Janairu p. 7

RAYUWAR KIRISTA

Ku Yi Shiri Yanzu don Jinyar Gaggawa

Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance a shirye? Jinyar gaggawa ta kan zo ba zato ba tsammani. Saboda haka, kafin yanayin gaggawa ya taso, yana da kyau mu kasance a shirye don mu sami kulawar da ta dace idan bukata ta taso. Yin hakan zai nuna mun daraja rai da kuma dokar Jehobah game da jini.​—A. M 15:​28, 29.

Me za mu iya yi don mu kasance a shirye?

  • Ku yi adduꞌa kuma ku cika Takardar Izinin Kula da Jinya (katin DPA).a Masu shela da suka yi baftisma za su iya samun katin daga wurin bawa mai kula da littattafai da kuma Katin Gabatarwa (ic) don yaransu

  • Mata masu juna biyu su gaya wa dattawan ikilisiyarsu su ba su takardar Information for Expectant Mothers (S-401). Takardar za ta taimaka musu su yanke shawarwari masu kyau game da duk wata matsalar da za ta iya tasowa a lokacin da suke da juna biyu da kuma lokacin haihuwa

  • Idan za a yi muku jinya da ta shafi batun jini ko kuma a kwantar da ku a asibiti, zai dace ku sanar da dattawa da wuri kuma ku gaya wa likitan cewa wani Mashaidi zai zo ya ziyarce ku

Ta yaya dattawa za su taimaka? Za su iya taimaka muku wajen cika katin DPA. Amma, dattawa ba za su yanke muku shawara game da jinya ba ko kuma su cusa muku raꞌayinsu game da shawarar da za ku yanke da kanku ba. (Ro 14:12; Ga 6:5) Idan kun sanar da dattawa cewa za ku yi jinyar da ta shafi batun jini, za su yi magana da Kwamitin Hulɗa da Asibitoci (HLC) nan da nan a madadinku.

Ta yaya HLC za su taimaka? An koyar da ꞌyanꞌuwan da suke hidima a HLC game da yadda za su taimaka wa likitoci da lauyoyi su fahimci raꞌayinmu game da batun jini. Za su iya tattaunawa da likitanku game da yadda zai iya yi muku jinya ba tare da jini ba. Idan da bukata, za su iya taimaka muku ku sami likitan da zai iya muku aiki ba tare da jini ba.

KU KALLI BIDIYON NAN TA YAYA ZA MU YANKE SHAWARWARI GAME DA JINYAR DA TA SHAFI JINI? SAI KU TATTAUNA TAMBAYA TA GABA:

  • Wane darasi ne kuka koya daga bidiyon nan da zai taimaka muku ku kasance a shirye saꞌad da kuke so ku yi jinyar gaggawa da ta shafi batun jini?

a Darasi na 39 na littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! zai taimaka muku ku san shawarar da za ku yanke game da batun da ya shafi jini.

A Shirye Kuke?

Saꞌad da kuke so ku yi jinyar da ta shafi batun jini,

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba