Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb22 Yuli p. 5
  • Ku Je Inda Ake Bukatar Masu Shela

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Je Inda Ake Bukatar Masu Shela
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Makamantan Littattafai
  • Mene Ne Ake Yi a Ofishin Reshe?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
  • Za Ka Iya “Ƙetaro Zuwa Makidoniya”?
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Shin Kana Koyon Dukan Abin da Za Ka Iya Koya Daga Wurin Jehobah?
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • “Ga Ni; Ka Aike Ni!”
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
mwb22 Yuli p. 5
Hotuna daga bidiyon “Ku Kara Kwazo a Hidimarku da Bangaskiya​—Ku Je Inda Ake Bukatar Masu Shela.” Hotuna: 1. Gabriel ya yi bincike. 2. Ya tattauna da wani dattijo game da yadda zai tura wa reshen ofishi sako. 3. Yana wa’azi da abokinsa Samuel a lokacin da ake wata wa’azi ta musamman.

RAYUWAR KIRISTA | KU KAFA MAƘASUDAI DON SABUWAR SHEKARA TA HIDIMA

Ku Je Inda Ake Bukatar Masu Shela

Kana bukatar ka kasance da bangaskiya kafin ka je wurin da ake bukatar masu shela. (Ibr 11:​8-10) Idan kana tunanin ƙaura zuwa inda ake bukatar masu shela, ka tattauna da dattawan ikilisiyarku. Mene ne za ka iya yi don ka san ko za ka iya cim ma wannan maƙasudin da kuma wurin da za ka je? Ka karanta littattafai da suka tattauna game da yin hidima a wurin da ake da bukata. Ka tattauna da waɗanda suka ƙaura zuwa ikilisiyar da ke bukatar taimako. (K. Ma 15:22) Ka yi addu’a don Jehobah ya taimaka maka. (Yak 1:5) Ka yi bincike sosai game da wurin da kake so ka koma kuma idan zai yiwu, ka kai ziyara wurin na ’yan kwanaki kafin ka yanke shawara.

KU KALLI BIDIYON NAN KU ƘARA ƘWAZO A HIDIMARKU DA BANGASKIYA​—KU JE INDA AKE BUKATAR MASU SHELA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Waɗanne canje-canje ne Gabriel ya yi? Kuma mene ne ya taimaka masa?

Idan kana so ka san game da ikilisiyoyin da ke kusa da kai da suke da bukata, ka tattauna da mai kula da da’irarku. Idan kana so ka san game da ikilisiyoyin da suke nesa da inda kake, ka rubuta wa reshen ofishi da ke kula da ikilisiyoyin ta wurin Kwamitin Hidima na Ikilisiyarku. Idan ba reshen ofishinku ba ne ke kula da ikilisiyoyin ba, sai ka rubuta wa reshen ofishin da ke kula da ikilisiyoyin da ke ƙasar. Idan kuma akwai wani wurin da ka fi so, za ka iya ambata hakan cikin wasiƙarka.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba