Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb21 Mayu p. 13
  • Ku Riƙa Nuna Ƙauna a Iyali

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Riƙa Nuna Ƙauna a Iyali
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Iyalinka Za Ta Zauna Lafiya
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Yadda Za Ka Sa Rayuwar Iyalinka ta Zama Mai Farin Ciki
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Rayuwar Iyali da ke Gamshe Allah
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
  • Iyalai Kirista, Ku Bi Misalin Yesu!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
mwb21 Mayu p. 13
Wata iyali tana rera waka tare a taro.

RAYUWAR KIRISTA

Ku Riƙa Nuna Ƙauna a Iyali

Ƙauna ce take ƙara danƙon zumunci a iyali. Idan babu ƙauna a iyali, ba za a kasance da zumunci da haɗin kai ba. Ta yaya maza da mata da kuma iyaye za su riƙa nuna ƙauna a iyali?

Maigidan da yake ƙaunar matarsa zai yi la’akari da bukatunta da ra’ayinta da kuma yadda take ji. (Afi 5:​28, 29) Zai kula da bukatun iyalinsa, kuma hakan ya ƙunshi taimaka musu su kusaci Jehobah. (1Ti 5:8) Matar da take ƙaunar mijinta za ta yi masa biyayya kuma ta “girmama” shi. (Afi 5:​22, 33; 1Bi 3:​1-6) Dole ne mata da miji su riƙa gafarta wa juna. (Afi 4:32) Iyayen da suke ƙaunar yaransu suna kula da kowanne cikin yaran kuma su koyar da su game da Jehobah. (M.Sh 6:​6, 7; Afi 6:4) Waɗanne matsaloli ne yaran suke fuskanta a makaranta? Yaya suke bi da matsi daga tsararsu? Idan akwai ƙauna a iyali, membobin iyalin za su sami kāriya da kwanciyar hankali.

KU KALLI BIDIYON NAN KU NUNA ƘAUNAR DA BA TA ƘAREWA A IYALINKU, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Wani hoto daga bidiyon nan ‘Ku Nuna Kaunar da Ba Ta Karewa a Iyalinku.’ Mata da miji suna tattauna nassi tare bayan sun dawo daga taro.

    Ta yaya maigida yake kula da matarsa kuma ya nuna cewa tana da daraja a gare shi?

  • Wani hoto daga bidiyon nan ‘Ku Nuna Kaunar da Ba Ta Karewa a Iyalinku.’ Bayan wata ’yar’uwa ta dawo daga taro, ta saurari maigidanta da ba Mashaidi ba kuma ta karfafa shi.

    Ta yaya matar kirki take nuna cewa tana girmama mijinta?

  • Wani hoto daga bidiyon nan ‘Ku Nuna Kaunar da Ba Ta Karewa a Iyalinku.’ Wata iyali tana tattauna abubuwan da ta koya daga taro yayin da suke cin abinci.

    Ta yaya iyaye suke koyar da yaransu Kalmar Allah?

HAƊARIN DA KE TATTARE DA NA’URORIN FASAHA

Yana da sauƙi iyalai su yi amfani da lokacin da ya kamata su kasance da juna wajen yin amfani da na’urorin fasaha. Ya kamata iyaye su rage yawan lokacin da su da yaransu suke kashewa wajen amfani da na’urorin fasaha. Ƙari ga haka, iyaye ne suke da hakkin tsai da shawara ko za su amince yaransu su yi amfani da hanyoyin sada zumunta na intane ko a’a da kuma irin mutanen da za su riƙa tattaunawa da su a dandalin sada zumunta.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba