Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb21 Janairu p. 7
  • Taron Yanki Yana Ba Mu Damar Nuna Ƙauna

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Taron Yanki Yana Ba Mu Damar Nuna Ƙauna
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah Yana Tattara Mutanensa Masu Farin Ciki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • “Yarensu Dabam Amma Ƙauna ta Haɗa Su”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Jehobah Ya San Abin da Muke Bukata
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
mwb21 Janairu p. 7

RAYUWAR KIRISTA

Taron Yanki Yana Ba Mu Damar Nuna Ƙauna

’Yan’uwa daga kasashe dabam-dabam da suka zo taron kasa da kasa suna daukan hoto.

Me ya sa muke jin daɗin taron yankin da muke yi a kowace shekara? Kamar yadda yake a zamanin Isra’ilawa, taron yankinmu yana ba mu damar bauta wa Jehobah tare da ’yan’uwanmu da yawa. Muna jin daɗin dukan bayanan da muke samu da suke sa mu ci gaba da kasance kusa da Jehobah. Ban da haka ma, muna jin daɗin yin tarayya da ’yan’uwa da abokan arziki. Shi ya sa mukan halarci taron na kwanaki uku don mu nuna godiyarmu.

Idan muka sami damar taruwa, kada mu mai da hankali ga abin da zai amfane mu kawai, amma mu nemi zarafi don mu nuna ma ’yan’uwanmu ƙauna. (Ga 6:10; Ibr 10:​24, 25) Idan muka keɓe wurin zama da muke bukata kawai kuma ba mu tare hanya da ’yan’uwanmu suke bi ba, hakan zai nuna cewa muna mai da hankali ga abin da zai amfani ’yan’uwanmu. (Fib 2:​3, 4) A taron yanki, muna samun damar yin sabbin abokai. Kafin ko kuma bayan an gama taro da kuma lokacin cin abinci da rana, za mu iya amfani da waɗannan zarafin mu nemi sabbin abokai. (2Ko 6:13) Idan mun yi abokantaka a lokacin taron yanki, abokantakarmu za ta iya kasance har abada! Abin da ya fi muhimmanci kuma shi ne idan mutane sun ga yadda muke nuna wa juna ƙauna, hakan zai iya sa su ma su soma bauta wa Jehobah.​—Yoh 13:35.

KU KALLI BIDIYON NAN TARON ƘASA DA ƘASA NA “ƘAUNA BA TA ƘAREWA”! SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Wani hoto da aka dauko daga bidiyon nan Taron Kasa da Kasa Na “Kauna Ba Ta Karewa”!’ ’Yan’uwa maza da mata suna murna suna gaisuwa a taron kasa da kasa.

    Ta yaya aka nuna ƙauna ga ’yan’uwa da suka halarci taron ƙasa da ƙasa na 2019?

  • Wani hoto da aka dauko daga bidiyon nan Taron Kasa da Kasa Na “Kauna Ba Ta Karewa”!’ ’Yan’uwa maza da mata da ke kasar da ma wadanda suka fito daga wasu kasashe suna daukan hoto.

    Me ya sa ƙauna da haɗin kai da ke tsakanin bayin Allah suke da ban sha’awa?

  • Wani hoto da aka dauko daga bidiyon nan Taron Kasa da Kasa Na “Kauna Ba Ta Karewa”!’ Wasu ’yan’uwa daga Koriya sun rike alamar marabtar baki kuma suna marabtar ’yan’uwa da suke zuwa taron.

    Wace irin ƙauna ta Kirista ce membobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu suka tattauna?

  • Wani hoto da aka dauko daga bidiyon nan Taron Kasa da Kasa Na “Kauna Ba Ta Karewa”!’ Wata yarinya ta rike juyin ‘New World Translation’ da aka fitar tana farin ciki.

    Ta yaya kai ma za ka nuna ƙauna a taron yanki?

    Ta yaya ’yan’uwanmu suka ci gaba da nuna ƙauna ba fasawa a ƙasar Jamus da Koriya ta Kudu?

  • Me ya kamata mu kudiri aniyar yi?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba