7-13 ga Satumba
FITOWA 23-24
Waƙa ta 34 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Kada Ka Bi Bayan Taron Jama’a”: (minti 10)
Fit 23:1—Kada ka yaɗa ƙarya (w18.08 4-5 sakin layi na 7-8)
Fit 23:2—Kada ka aikata mugunta domin yawancin mutane suna yin hakan (mwbr20.09-HA an ɗauko daga it-1 11 sakin layi na 3)
Fit 23:3—Kada ka nuna bambanci (mwbr20.09-HA an ɗauko daga it-1 343 sakin layi na 5)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 10)
Fit 23:9—Mene ne Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa don ya sa su zama masu jin tausayi? (w16.10 9 sakin layi na 4)
Fit 23:20, 21—Me ya sa muka tabbata cewa mala’ikan da aka yi maganarsa a ayoyin nan Mika’ilu ne? (mwbr20.09-HA an ɗauko daga it-2 393)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da wa’azi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Fit 23:1-19 (th darasi na 5)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Bidiyon Haɗuwa ta Fari: (minti 4) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon sai ku amsa waɗannan tambayoyin: Mene ne mai shelar ta yi sa’ad da matar ta ba da amsar da ba daidai ba? Ta yaya za ka ba da Hasumiyar Tsaro ta 3, 2020 a wannan yanayin?
Haɗuwa ta Fari: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka soma da bin bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Sai ka gabatar da kuma tattauna (amma kar ka kunna) bidiyon nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? (th darasi na 1)
Jawabi: (minti 5 ko ƙasa da hakan) w16.05 30-31—Jigo: Mene ne Zai Taimaka wa Kiristoci Su San Ko Ya Dace Su Ba da Kyautar Kuɗi Ko Kuma Wani Abu ga Ma’aikatan Gwamnati? (th darasi na 14)
RAYUWAR KIRISTA
“Ka Guji Yaɗa Ƙarya”: (minti 15) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon zanen allon nan Ta Yaya Zan Guji Yaɗa Gulma?
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30 ko ƙasa da hakan) ia babi na 16 sakin layi na 16-29 da akwatin da ke shafi na 142 da kuma Taƙaitawa da ke shafi na 144
Kammalawa (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Waƙa ta 145 da Addu’a