Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb20 Yuli p. 7
  • Jehobah Yana Kāre Mutanensa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Yana Kāre Mutanensa
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • Makamantan Littattafai
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Kana “Ganin Wanda Ba Shi Ganuwa” Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Maganar Jehobah Tana Cika A Kullayaumi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ku Ci-gaba da Bin Ja-gorancin Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
mwb20 Yuli p. 7

RAYUWAR KIRISTA

Jehobah Yana Kāre Mutanensa

Wani Ba-isra’ile da dansa suna yayyafa jini a saman kofar gidansu.

Idin Ƙetarewa na farko da aka yi yana da muhimmanci sosai. Da Fir’auna ya ga cewa ɗan farinsa ya mutu a daren, sai ya kira Musa ya ce: “Tashi! Ku fita ku bar mutanena, ku da jama’arku Isra’ila! Ku tafi ku yi wa Yahweh sujada, kamar yadda kuka faɗa.” (Fit 12:31) Wannan abin da Jehobah ya yi ya nuna cewa yana kāre mutanensa.

Idan muka bincika tarihin Shaidun Jehobah a yau, za mu gane cewa a kullum Jehobah yana ja-gorar mutanensa kuma yana kāre su. An nuna hakan a wurin adana kayayyakin tarihi da ke hedkwatarmu mai jigo, “A People for Jehovah’s Name.”

KU KALLI BIDIYON NAN ZAGAYA WURIN ADANA KAYAKIN TARIHI: “A PEOPLE FOR JEHOVAH’S NAME,” SA’AN NAN KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Hotunan da aka dauko daga bidiyon nan ‘Photo-Drama of Creation.’

    Wane abu ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka yi amfani da shi a farkon 1914 don mutane su ƙara gaskata da Littafi Mai Tsarki, kuma ta yaya suka yi nasara?

  • Hotunan ’yan’uwa da aka kama kuma aka saka su a kurkuku a shekara ta 1918.

    Waɗanne matsaloli ne suka fuskanta a 1914 da 1918, kuma me ya nuna cewa Jehobah ne yake wa ƙungiyarmu ja-gora?

  • Wasu hotuna a wurin adana kayayyakin tarihi da suka nuna mutane da yawa da aka saka su a kurkuku don imaninsu. Kofa ta bude dakin da aka zana hoton aljanna.

    Ta yaya bayin Jehobah suka jimre sa’ad da maƙiyansu suka yi adawa da su?

  • Wani wurin adana kayayyakin tarihi da yake nuna abubuwan da aka yi amfani da su don wa’azi daga shekara ta 1930 zuwa 1949.

    Wane ƙarin haske ne bayin Jehobah suka samu a shekara ta 1935, kuma ta yaya hakan ya shafe su?

  • Idan ka taɓa zuwa wurin adana kayayyakin tarihin nan, me ka gani da ya tabbatar maka cewa Jehobah ne yake ja-gorar mutanensa kuma yana kāre su?

Don ka san yadda za ka iya zuwa wurin adana kayayyakin tarihinmu, ka shiga dandalin jw.org® kuma ka danna Game da Mu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba