DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FARAWA 48-50
Za Mu Iya Koyan Abubuwa Daga Tsofaffi
48:21, 22; 49:1; 50:24, 25
Idan tsofaffi suka gaya mana labaran yadda Jehobah ya yi ‘ayyuka na ban mamaki’ a wannan zamani na ƙarshe, hakan yana ƙarfafa bangaskiyarmu. (Za 71:17, 18) Idan akwai waɗanda suka daɗe suna bauta wa Jehobah a ikilisiyarku, ka tambaye su
yadda Jehobah ya taimaka musu su jimre matsaloli
yaya suka ji game da yadda ’yan’uwa suka ƙaru
yadda suka ji game da ƙarin haske da ƙungiyarmu take samuwa
yadda suka ji game da ci gaban da ƙungiyarmu take samuwa