Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb20 Afrilu p. 7
  • Ku “Kawar da Gumakan Allolin” Karya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku “Kawar da Gumakan Allolin” Karya
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah Yana Taimaka Mana Mu Yi Tsayayya da Mugayen Ruhohi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Mu Bauta wa Jehobah da Dukan Zuciyarmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Yakubu da Isuwa Sun Shirya
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Ka Zabi Nishadi da Zai Faranta Ran Jehobah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
mwb20 Afrilu p. 7
Wani mutum yana yar da abin wuya da ke da alaka da sihiri.

RAYUWAR KIRISTA

Ku “Kawar da Gumakan Allolin” Ƙarya

Yakub ya san cewa Jehobah ne kaɗai ya kamata a bauta wa, ko da yake a lokacin Jehobah bai kafa doka game da bautar gumaka ba. (Fit 20:​3-5) Shi ya sa bayan da Jehobah ya gaya wa Yakub ya koma Betel, Yakub ya gaya ma waɗanda suke tare da shi su kawar da dukan gumaka da suke wurinsu. Yakub ya binne gumakan har da ’yan kunne da suke sakawa don samun kāriya. (Fa 35:​1-4) Babu shakka, Jehobah ya ji daɗin matakin da Yakub ya ɗauka.

A yau, ta yaya za mu bauta wa Jehobah shi kaɗai? Muna bukatar mu guje wa duk wani abin da yake da alaƙa da bautar gumaka da kuma sihiri. Hakan na nufin za mu kawar da abubuwan tsafi kuma mu riƙa zaɓan nishaɗin da za mu yi. Alal misali, ka tambayi kanka: ‘Ina jin daɗin karanta littattafai ko kuma kallon fina-finan da suke nuna maita, aljanu ko kuma dodanni? Nishaɗin da nake yi yana nuna cewa tsafi da bokanci da kuma yi wa mutane asiri ba laifi ba ne? Ya kamata mu nisanta kanmu daga duk abin da Jehobah ya tsana.​—Za 97:10.

KU KALLI BIDIYON NAN “KADA KU BA SHAIƊAN DAMA,” SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Wani jariri da aka saka masa layu a hannunsa yana kwance a kan gado. Ga mahaifiyarsa a baya tana tattauna da wasu ma’aurata da suke nazarin Littafi Mai Tsarki da ita.

    Wace matsala ce wata ɗaliban Littafi Mai Tsarki mai suna Palesa ta soma fuskanta?

  • Ma’auratan da dalibar suna tattaunawa da dattawa don ta sami taimako.

    Me ya sa yake da kyau mu nemi taimakon dattawa idan mu ko ɗalibinmu yana da matsalar da ta shafi sihiri?

  • Dalibar tana kona layar yaronta a wuta.

    Kada ka ba Shaiɗan dama kuma ka yi kusa da Allah. ​—Yaƙ 4:​7, 8

    Waɗanne abubuwa ne muke bukatar mu kawar da su idan muna so Jehobah ya kāre mu?

  • Wane mataki mai kyau ne Palesa ta ɗauka?

  • Mene ne za ka iya yi a yankinku don ka guji abubuwan da suka shafi aljanu?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba