DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | RU’UYAR DA AKA YI WA YOHANNA 13-16
Kada Ku Ji Tsoron Dabbobin Nan Masu Ban Tsoro
13:1, 2, 11, 15-17
Idan muka fahimci abin da dabbobin da ke littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna sura 13 suke wakilta, hakan zai taimaka mana mu daina jin tsoron su ko kuma mu goyi bayansu kamar yadda sauran mutane suke yi.
Ka Nuna Abin da Dabbobin Nan Suke Wakilta
DABBOBI
Dodon nan mai siffar maciji.—R. Yar 13:1
Dabba mai ƙahoni goma da kuma kawuna bakwai.—R. Yar 13:1, 2
Dabba mai ƙahoni biyu kamar na ɗan rago.—R. Yar 13:11
Siffar dabba ta farko.—R. Yar 13:15
MULKOKI
Mulkin Biritaniya da Amirka
Majalisar Ɗinkin Duniya ta dā da kuma ta yanzu
Shaiɗan Iblis
Dukan gwamnatocin da suke hamayya da Allah