RAYUWAR KIRISTA
Yadda Muka Ba da Agaji ga ’Yan’uwanmu a Karibiya
Kamar yadda Kiristoci a ƙarni na farko suka taimaka wa ’yan’uwa masu bi da bala’i ya shafa, mu ma a yau za mu iya yin hakan. (Yoh 13:34, 35) Ku kalli bidiyon nan Yadda Muka Nuna Ƙauna ta Wajen Kai Agaji a Karibiya don ku ga yadda ’yan’uwa suka taimaka ma Shaidu da bala’i ya shafa a Karibiya. Bayan haka, ku amsa tambayoyin nan:
Ta yaya guguwa da aka yi a Karibiya ta shafi ’yan’uwanmu?
Ta yaya Jehobah ya yi amfani da ’yan’uwa maza da mata don ya taimaka wa ’yan’uwanmu da ke Karibiya?
Ta yaya waɗanda guguwa ta shafa suka amfana daga taimakon da ’yan’uwanmu suka ba su?
’Yan’uwa guda nawa ne suka yi aikin agaji a Karibiya?
Ta yaya kowannenmu zai iya taimakawa a aikin agaji?
Da ka kalli bidiyon nan, yaya ka ji game da kasancewa cikin wannan ƙungiyar?