DARUSSA DAGA LITTAFI MAI TSARKI | ROMAWA 12-14
Yadda Za Mu Nuna Ƙauna ga ’Yan’uwa
Idan muna ƙaunar ’yan’uwanmu, ba za mu rama laifin da suka yi mana ba, sai dai mu sāka musu da alheri. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan abokin gābanka yana jin yunwa, sai ka ba shi abinci. Idan yana jin ƙishin ruwa, sai ka ba shi ruwan sha. Ta yin haka kana tara garwashin wuta a kansa ne.” (Ro 12:20) Alherin da muka nuna wa mutumin da ya yi mana laifi zai iya sa ya yi da-na-sani.
Yaya ka ji sa’ad da ka yi ma wani laifi cikin rashin sani amma bai rama ba kuma ya yi maka alheri?