Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb19 Fabrairu p. 8
  • Ku Rika Jira da Hakuri

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Rika Jira da Hakuri
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Makamantan Littattafai
  • Kada Ka Bar Wani Abu Ya Hana Ka Samun Ladar
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • ‘Bari Hakuri Ya Cika Aikinsa’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Jehobah Yana Taimaka Mana Saꞌad da Muke Cikin Matsala
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
mwb19 Fabrairu p. 8

RAYUWAR KIRISTA

Ku Riƙa Jira da Haƙuri

Shekaru nawa ka yi kana jiran Mulkin Allah ya zo? Kana kan jira da haƙuri duk da matsalolin da kake fuskanta? (Ro 8:25) Wasu Kiristoci suna fuskantar ƙiyayya da kuma wulakanci. Wasu kuma an saka su a fursuna har ma ana barazanar cewa za a kashe su. Har ila, wasu suna fama da ciwo ko kuma tsufa.

Me zai taimaka mana mu riƙa jira da marmari duk da matsalolin da muke fama da su? Wajibi ne mu riƙa ƙarfafa bangaskiyarmu a kullum ta wurin karanta Kalmar Allah da kuma yin bimbini a kan abin da muka karanta. Zai dace mu mai da hankali a kan abin da muke begen sa. (2Ko 4:​16-18; Ibr 12:2) Ƙari ga haka, ya kamata mu yi addu’a ga Jehobah kuma mu roƙe shi ya taimaka mana da ruhunsa mai tsarki. (Lu 11:​10, 13; Ibr 5:7) Idan muka yi hakan, Ubanmu mai ƙauna zai taimaka mana mu ‘jimre kowane abin da ya faru muna haƙuri da farin ciki.’​—Kol 1:11.

KU KALLI BIDIYON NAN WAJIBI NE KU YI TSERE DA JIMIRI​—KU KASANCE DA TABBACIN SAMUN LADAN, BAYAN HAKA, KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Jamie da matarsa suna wa’azi

    Waɗanne abubuwa ne za mu iya fuskanta ba zato ba labari? (M. Wa 9:11)

  • Carl yana karanta wa Jamie wani nassi bayan Jamie ya kamu da cutar shanyewar jiki

    Ta yaya addu’a za ta taimaka mana sa’ad da muke fuskantar matsaloli?

  • Jamie da Carl suna karfafa wasu ma’aurata

    Idan ba ma iya yin abubuwan da muka saba yi a hidimarmu ga Jehobah, me ya sa zai dace mu mai da hankali a kan abin da za mu iya yi?

  • Jamie yana tunanin yadda zai kasance da lafiyar jiki a Aljanna

    Ka mai da hankali ga abin da kake begen sa

    Me yake taimaka maka ka kasance da tabbaci cewa za ka sami ladan?

Ta yaya za ka taimaka ma waɗanda suke fuskantar matsaloli har da iyalinsu?

  • Ka riƙa musu magana da ladabi kuma kar ka gwada abin da suke yi da na wasu

  • Ka riƙa saurarar su da kyau

  • Ka yi addu’a tare da su da kuma a madadinsu

  • Ka dafa musu abinci ko kuma ka taya su yin wasu ayyuka

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba