Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb19 Janairu p. 7
  • ‘Bulus Ya Yi Godiya Ga Allah Kuma Ya Sami Karfin Gwiwa’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Bulus Ya Yi Godiya Ga Allah Kuma Ya Sami Karfin Gwiwa’
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Makamantan Littattafai
  • Suna Aiki Tuƙuru don Su Taimaka Mana
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Yaya Masu Kula Masu Ziyara Suke Taimaka Mana?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
mwb19 Janairu p. 7
Bulus ya yi godiya ga Allah domin ’yan’uwa da suka yi tafiya mai nisa don su marabce shi

RAYUWAR KIRISTA

‘Bulus Ya Yi Godiya Ga Allah Kuma Ya Sami Ƙarfin Gwiwa’

Da ikilisiyar da ke Roma ta ji cewa Bulus yana zuwa, wasu ’yan’uwa sun yi tafiya na wajen kilomita 64 don su marabce shi. Hakan ya ƙarfafa Bulus kuwa? Littafi Mai Tsarki ya ce, “Da Bulus ya gan su kuwa ya yi godiya ga Allah, ya kuma ƙara samun ƙarfin gwiwa.” (A. M 28:15) Ko da yake Bulus yana ƙarfafa ’yan’uwa a ikilisiyoyin da ya je, a wannan karon da aka kama shi, ’yan’uwan ne suka ƙarfafa shi.​—2Ko 13:10.

A yau, masu kula da da’ira suna zuwa ikilisiyoyi da yawa don su ƙarfafa mu. Kamar dukan bayin Jehobah, su ma a wasu lokuta suna fuskantar matsaloli kamar gajiya da damuwa da kuma sanyin giwa. Don haka, idan mai kula da da’ira da matarsa suka sake zuwa ikilisiyarku, mene ne za ka iya yi don dukanku ‘ku ƙarfafa juna’?​—Ro 1:​11, 12.

  • Wani mai kula da da’ira yana gudanar da taron fita wa’azi

    Ka fita wa’azi a makon da mai kula da da’ira ya zo. Mai kula da da’ira yana farin ciki sosai idan ya ga ƙoƙarin da masu shela suke yi don su fita wa’azi in ya ziyarce su. (1Ta 1:​2, 3; 2:20) Kana iya yin hidimar majagaba na ɗan lokaci a watan da zai zo. Kana iya yin wa’azi tare da shi ko matarsa ko kuma ka kai shi ko matarsa wurin ɗalibanka don ku yi nazari. Shi da matarsa suna son yin wa’azi tare da masu shela dabam-dabam har da waɗanda ba su daɗe da zama masu shela ba da kuma waɗanda suke ganin ba su iya wa’azi sosai ba.

  • Wata iyali ta marabce wani mai kula da’ari da matarsa

    Ka nuna musu karimci. Kana iya ba su wurin kwanciya ko kuma abinci. Hakan zai sa mai kula da da’irar da matarsa su fahimci cewa kana ƙaunar su. Kuma ba sai ka kashe kuɗi sosai a kan su ba.​—Lu 10:​38-42.

  • Wani mai kula da da’ira yana gudanar da taro tare da dattawa

    Ka yi amfani da shawarwarin da ya ba ka. Masu kula da da’ira suna taimaka mana mu bauta wa Jehobah da kyau sosai. A wasu lokuta, za su iya ja mana kunne. (1Ko 5:​1-5) Suna farin ciki sosai idan suka ga muna yin abin da suka gaya mana.​—Ibr 13:17.

  • ’Yan’uwa a ikilisiya suna godiya ga mai kula da da’ira da matarsa

    Ka gode musu. Ka gaya wa mai kula da da’ira da matarsa yadda ka amfana daga ƙoƙarin da suke yi. Za ka iya yin haka ta wurin rubuta masa gajeren wasiƙa ko kuma ka gaya masa da baki.​—Kol 3:15.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba