24-30 ga Satumba
YOHANNA 7-8
Waƙa ta 12 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Yesu Ya Ɗaukaka Ubansa”: (minti 10)
Yoh 7:15-18—Idan aka yaba wa Yesu don koyarwarsa, yakan gaya musu cewa koyarwarsa daga Jehobah ne (mwbr18.09-HA an ɗauko daga cf 100-101 sakin layi na 5-6)
Yoh 7:28, 29—Yesu ya ce shi wakilin Jehobah ne kuma hakan ya nuna cewa Jehobah ya fi shi iko
Yoh 8:29—Yesu ya gaya wa masu sauraronsa cewa a kullum yana yin abin da zai faranta wa Jehobah rai (w11 3/15 11 sakin layi na 19)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Yoh 7:8-10—Shin abin da Yesu ya faɗa wa ’yan’uwansa da ba almajiransa ba ƙarya ne? (w07 2/1 6 sakin layi na 4)
Yoh 8:58—Me ya sa a ayar nan muka yi amfani da furucin nan “Ina nan” maimakon “Ni ne,” kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci? (mwbr18.09-HA an ɗauko daga nwtsty)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Yoh 8:31-47
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Komawa Ziyara ta Biyu: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka fara da bin bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Sai ka gayyaci mutumin zuwa taro.
Komawa Ziyara ta Uku: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka zaɓi nassin da za ka yi amfani da shi kuma ka ba shi ɗaya daga cikin littattafan da muke amfani da su don nazari.
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) lv babi na 1 sakin layi na 10-11
RAYUWAR KIRISTA
“Ku Kasance da Sauƙin Kai da Sanin Yakamata Kamar Yesu”: (minti 15) Tattaunawa. Ka saka kowane bidiyon.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 13 sakin layi na 5-15 da kuma akwatin da ke shafi na 150
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 119 da Addu’a