Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb18 Agusta p. 7
  • Ba Don Kai Kadai Yesu Ya Mutu Ba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ba Don Kai Kadai Yesu Ya Mutu Ba
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Kasance da Hadin Kai a Ikilisiya
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ka Kasance Da Hali Irin Na Kristi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Kada Ka Sa “Yara Kananan Nan” Tuntube
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
mwb18 Agusta p. 7
Yesu yana wa mabiyansa magana

RAYUWAR KIRISTA

Ba Don Kai Kaɗai Yesu Ya Mutu Ba

Yesu ya mutu a madadin ’yan Adam ajizai. (Ro 5:8) Hakika, muna wa Yesu matuƙar godiya don abin da ya yi mana. Amma a wasu lokuta, muna bukatar mu riƙa tuna cewa ba don mu kaɗai ne Yesu ya mutu ba, amma har da ’yan’uwanmu. Ta yaya za mu ƙaunaci ’yan’uwanmu ajizai kamar yadda Yesu ya yi? Na farko, mu riƙa yin abokanta da mutane dabam-dabam ba kawai waɗanda ala’adarmu ɗaya ba. (Ro 15:7; 2Ko 6:​12, 13) Na biyu, mu mai da hankali sosai don kada mu yi ko faɗi abubuwan da za su ɓata ma wasu rai. (Ro 14:​13-15) Na uku shi ne, mu riƙa saurin gafarta wa ’yan’uwanmu idan suka yi mana laifi. (Lu 17:​3, 4; 23:34) Idan muna yin hakan, Jehobah zai sa mu kasance da salama da kuma haɗin kai a ikilisiya.

KU KALLI BIDIYON NAN KA KYAUTATA HALINKA!, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • ’Yan’uwa a ikilisiyarsu Miki sun marabce ta

    Yaya ’Yar’uwa Miki ta ji da farko game da ’yan’uwan da ke ikilisiyarsu?

  • ’Yan’uwa a ikilisiyarsu Miki suna bata mata rai

    Me ya sa ta canja ra’ayinta?

  • Duk da cewa manzannin Yesu sun yi barci, Yesu ya nuna musu alheri

    Ta yaya misalin Yesu ya taimaka wa ’Yar’uwa Miki ta canja ra’ayinta? (Mk 14:38)

  • Miki ta yi dariya sa’ad da wani yaro ya buge ta har ya sa ta zubar da ruwan da take sha a jikinta

    Ta yaya Misalai 19:11 take taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace game da ’yan’uwanmu?

DON BIMBINI:

Ina fushi da ’yan’uwana a kan laifin da suka yi min da bai taka kara ya karya ba?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba