DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | LUKA 17-18
Ku Riƙa Nuna Godiya
Me wannan labarin ya koya mana game da nuna godiya?
Mu gode wa mutane sa’ad da suka yi mana wani abu mai kyau
Idan muna gode wa mutane daga zuciyarmu, hakan zai nuna cewa muna da halin kirki kuma muna ƙaunar su sosai
Waɗanda suke so su sa Kristi farin ciki suna bukatar su riƙa gode wa dukan mutane