4-10 ga Disamba
ZAFANIYA 1–HAGGAI 2
Waƙa ta 151 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Ku Biɗi Jehobah Kafin Ranar Fushinsa”: (minti 10)
[Ka saka bidiyon Gabatarwar Littafin Zafaniya..]
Zaf 2:2, 3—Ku biɗi Jehobah, ku biɗi adalci da kuma tawali’u (w01 3/1 10-11 sakin layi na 5-7)
[Ka saka bidiyon Gabatarwar Littafin Haggai..]
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Zaf 1:8—Wane gargaɗi ne ke cikin wannan ayar? (w07 12/1 15 sakin layi na 3)
Hag 2:9—A waɗanne hanyoyi ne haikalin Zerubabel ya fi na Sulemanu ɗaukaka? (w07 12/1 17 sakin layi na 2)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Hag 2:1-14
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Ka Shirya Gabatarwa na Wannan Watan: (minti 15) Tattauna “Gabatarwa” na wannan watan. Ka saka bidiyon gabatarwar mujallu, sai ka tattauna wasu abubuwa a ciki. Ka ƙarfafa masu shela su yi iya ƙoƙarinsu wajen rarraba mujallar Awake! Na 6 2017. Tun da mun fi so mu tattauna da mutane, kada mu bar wannan mujallar a gidajen da masu gidan ba sa nan.
RAYUWAR KIRISTA
Bukatun Ikilisiya: (minti 5)
Harshe Mai Tsarki Yana Kawo Haɗin Kai da Salama (Zaf 3:9): (minti 10) Tattaunawa da aka ɗauko daga Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Agusta 2012, shafi na 12, sakin layi na 4. Ka saka bidiyon nan Maƙiya da Suka Zama Abokai.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) kr babi na 22 sakin layi na 8-16
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 136 da Addu’a