Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb17 Oktoba p. 3
  • Yadda Za Ka Iya Yin Nazari Mai Zurfi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Ka Iya Yin Nazari Mai Zurfi
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Mai Da Hankali Ga Kalmomin Annabci Na Allah Don Kwanakinmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ku Zauna da Shiri Ta Wurin Yin Nazari Sosai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Kana Bauta wa Jehobah a Koyaushe?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Darussa Daga Littafin Daniel
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
mwb17 Oktoba p. 3

RAYUWAR KIRISTA

Yadda Za Ka Iya Yin Nazari Mai Zurfi

Kamar Daniyel, za ka so ka riƙe amincinka sa’ad da aka jarraba ka? Daniyel ya yi nazari mai zurfi na Kalmar Allah har da annabci masu wuya sosai. (Da 9:⁠2) Za ka iya riƙe amincinka idan kana nazari mai zurfi na Littafi Mai Tsarki. Ta yaya? Nazari zai sa ka ƙara gaskata da alkawuran Allah. (Jos 23:14) Zai sa ka ƙaunaci Allah sosai, kuma za ka riƙa yin abin da ya dace. (Za 97:10) Amma daga ina za ka soma nazarin? Ka lura da waɗannan shawarwarin.

Daniyel yana nazarin Kalmar Allah
  • Mene ne zan yi nazari a kai? Nazari mai kyau ya haɗa da yin shiri don taro. Za ka ji daɗin karatun Littafi Mai Tsarki da ake yi kowane mako idan kana nazari da kuma bincika abubuwan da ba ka gane ba. Ban da haka, wasu suna yin nazarin annabcin Littafi Mai Tsarki ko ’ya’yan ruhu mai tsarki ko tafiye-tafiyen da Bulus ya yi ko kuma halittun Jehobah. Idan ka yi tunani a kan wata tambaya ta Littafi Mai Tsarki, ka rubuta ta a ranar kuma ka sa ta zama abin da za ka yi bincike a kai.

  • Da mene ne zan yi bincike? Don ka ga wasu cikinsu, ka kalli bidiyon nan Kayan Bincike Don Nazarin Littafi Mai Tsarki. Ka yi bincike a kan dabbobin da aka ambata a Daniyel sura 7 don ka san mulkokin da dabbobin suke wakilta.

  • Awa nawa ne zan yi ina nazari? Yin nazari a kai a kai yana ƙarfafa dangantakarmu da Allah. Da farko, kana iya amfani da gajeren lokaci wajen yin nazari. Daga baya, kana iya ƙara yawan lokacin da kake amfani da shi. Yin nazarin Kalmar Allah kamar neman gwal yake. Idan kana samun bayanai masu tamani, za ka ci gaba da nema! (Mis 2:​3-6) Za ka so Kalmar Allah sosai kuma za ka riƙa nazarinta a kai a kai.​—⁠1Bi 2:⁠2.

    Don ƙari bayani a kan yadda za ka ji daɗin nazarin Littafi Mai Tsarki, ka duba shafi na 18-20 na Awake! ɗin watan Fabrairu 2012.

MENE NE DABBOBIN DA KE DANIYEL SURA 7 SUKE WAKILTA?

  • Wata dabba mai kama da zaki kuma tana da fukafukai kamar na gaggafa

    Da 7:4

  • Wata dabba mai kama da bear kuma akwai kasusuwa uku a bakinta

    Da 7:5

  • Wata dabba mai kama da damisa, tana da kawuna hudu da kuma fukafukai hudu a bayanta

    Da 7:6

  • Wata dabba mai ban tsoro da ke da hakorin karfe da kuma kaho guda goma

    Da 7:7

ƘARIN TAMBAYA:

Ta yaya Daniyel 7:​8, 24 suka cika?

Wani karamin kaho da ke da ido, kuma wani karamin baki ya fito a cikin koho na goman kuma ya cire kaho guda uku

AIKI NA GABA:

Mene ne dabbobin da ke Ru’ya ta Yohanna sura 13 suke wakilta?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba