RAYUWAR KIRISTA
Za Ka Yafe wa Kanka Kuwa?
Sa’ad da muka yi zunubi, yana iya mana wuya mu gafarta wa kanmu duk da cewa Jehobah ya riga ya gafarta mana. An tattauna wannan batun a wani jawabi da kuma bidiyo a Taron Yanki na shekara ta 2016, mai jigo “Ka Riƙe Aminci ga Jehobah!” Ku yi amfani da manhajar JW Library don ku sake kallon bidiyon, sai ku amsa waɗannan tambayoyin:
Shekaru nawa ne aka yi wa Sonja yanka zumunci?
Wane nassi ne dattawa suka karanta wa Sonja, kuma ta yaya hakan ya taimaka mata?
Mene ne ’yan’uwa a ikilisiya suka yi sa’ad da aka maido da Sonja?
Wane tunani ne Sonja ta yi fama da shi, kuma ta yaya mahaifinta ya taimaka mata?