DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MISALAI 7-11
“Kada Ka Bar Zuciyarka ta Karkata”
Ƙa’idodin Jehobah za su kāre mu a yau. Don mu amfana, muna bukatar mu riƙe su a zuciyarmu. (Mis 7:3) Idan bawan Jehobah ya karkata zuciyarsa daga bin ƙa’idodin Jehobah, zai kasance da sauƙi shaiɗan ya yaudare shi da dabarunsa. Misalai sura 7 ya kwatanta yadda wani saurayi ya ƙyale zuciyarsa ta yaudare shi. Mene ne za mu iya koya daga kuskurensa?
Gani
7:10
Taɓawa
7:13
Ɗanɗana
7:14
Sansana
7:17
Ji
7:21
Shaiɗan yana ƙoƙari ya hana mu bauta wa Jehobah ta wajen yin amfani da gaɓoɓin jikinmu guda biyar
Hikima da kuma fahimi za su taimaka mana mu san illar yin zunubi da kuma yadda za mu guji yin zunubi