12-18 ga Satumba
ZABURA 120-134
Waƙa ta 33 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Daga Wurin Ubangiji Taimakona Yake Fitowa”: (minti 10)
Za 121:1, 2—Muna dogara ga Jehobah don shi ya halicci kome (w05 1/1 8 sakin layi na 3)
Za 121:3, 4—Jehobah yana biyan bukatun bayinsa (w05 1/1 9 sakin layi na 4)
Za 121:5-8—Jehobah yana kula da bayinsa a koyaushe (w05 1/1 9 sakin layi na 5-7)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Za 123:2—Mene ne ma’anar kwatanci na “idanun bayi”? (w06 9/1 30 sakin layi na 4)
Za 133:1-3—Wane darasi muka koya daga wannan zaburar? (w06 9/1 31 sakin layi na 2)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya mini game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne na koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon da zan iya yin amfani da su a wa’azi?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Za 127:1–129:8
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) Bangon gaba wp16.5—Yadda za mu bi da maigidan da ke hasala.
Koma Ziyara: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Bangon gaba wp16.5—Ka gayyaci mutumin zuwa taronmu.
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) fg darasi na 8 sakin layi na 6—Ka taimaki ɗalibin ya yi amfani da abin da yake koya.
RAYUWAR KIRISTA
Waƙa ta 114
Jehobah Ya Taimaka Mini Sosai: (minti 15) Ka saka bidiyon nan da ke jw.org/ha. (Ka shiga GAME DA MU > AYYUKA.) Ka tattauna tambayoyin nan: Ta yaya Jehobah ya taimaka wa Crystal, kuma yaya hakan ya ƙarfafa ta? Me take yi sa’ad da take wani tunanin da bai dace ba? Wane darasi ka koya daga labarinta?
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) ia Kammalawa sakin layi na 1-13
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 119 da Addu’a