Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb16 Afrilu p. 3
  • Ka Karfafa Wasu da Furuci Mai Kyau

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Karfafa Wasu da Furuci Mai Kyau
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Makamantan Littattafai
  • “Ba Zan Daina Tsare Mutuncina Ba!”
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
  • Jehobah Ya Warkar da Shi
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
  • Ayuba Ya Ɗaukaka Sunan Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Darussa Daga Littafin Ayuba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
mwb16 Afrilu p. 3

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYUBA 16-20

Ka Ƙarfafa Wasu da Furuci Mai Kyau

Ya kamata furucin mai ba da shawara ya zama mai ban ƙarfafa

16:4, 5

  • Ayuba ya bukaci taimako da kuma ƙarfafawa domin ya yi baƙin ciki da kuma sanyin gwiwa

  • Abokan Ayuba uku ba su ƙarfafa shi ba. Maimakon haka, sun zargi Ayuba kuma hakan ya daɗa sa shi baƙin ciki

Baƙar maganar da Bildad ya yi wa Ayuba ta sa shi kuka

19:2, 25

  • Ayuba ya roƙi Allah ya sauƙaƙa matsalolinsa, ko da zai mutu

  • Ayuba ya mai da hankali a kan begen tashin matattu kuma hakan ya sa ya ci gaba da jimrewa

Eliphaz yana magana da Ayuba yayin da Bildad da Zophar suke kallo

MASU ZARGIN AYUBA

Eliphaz

Eliphaz:

  • Wataƙila shi Ba-temane ne daga ƙasar Edom. A littafin Irmiya 49:​7, an ce ‘Yan Teman mutane ne masu hikima sosai

  • Wataƙila Eliphaz ne ya fi girma da shahara a cikin ‘masu-ta’aziyan’ kuma shi ya fara magana. Ya yi magana sau uku kuma maganganunsa sun fi ta sauran daɗewa

Zargin ƙarya:

  • Ya zargi amincin Ayuba kuma ya ce Allah bai amince da bayinsa ba (Ayu 4; 5)

  • Ya yi da’awar cewa Ayuba mai girman kai ne da mugu kuma ya ce ba ya tsoron Allah (Ayu 15)

  • Ya ce Ayuba mai haɗama ne da marar adalci kuma ya ce Allah ba ya daraja mutane (Ayu 22)

Bildad

Bildad:

  • Ba-shuhi. Wataƙila ya zauna kusa da Kogin Yufiretis

  • Shi ne na biyu da ya yi magana. Maganganun da ya yi sau uku sun fi gajarta kuma sun fi na Eliphaz zafi

Zargin ƙarya:

  • Ya zargi ‘ya’yan Ayuba da yin zunubi kuma sun cancanci bala’in da ya faɗa musu. Ya kuma ce Ayuba ba ya tsoron Allah (Ayu 8)

  • Ya ce Ayuba mai aikata laifi ne (Ayu 18)

  • Ya ce amincin ‘yan Adam aikin banza ne (Ayu 25)

Zophar

Zophar:

  • Shi Ba-na’amathi ne, wataƙila daga arewa maso yammacin Arabiya

  • Shi ne na uku da ya yi magana kuma maganarsa ce ta fi muni. Ya yi magana sau biyu kawai

Zargin ƙarya:

  • Ya zargi Ayuba da yin maganganun banza kuma ya ce ya daina miyagun ayyuka (Ayu 11)

  • Yana da’awar cewa Ayuba mugu ne kuma yana jin daɗin yin zunubi (Ayu 20)

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba