Gabatarwa
Hasumiyar Tsaro Yuli–Agusta
“Kana gani cewa wannan annabcin Littafi Mai Tsarki yana cika a yau kuwa? [Karanta Matta 24:11. Sai ka bari ya ba da amsa.] Talifin da ya soma daga shafi na 14 na wannan mujallar ya tattauna yadda za mu gane annabawan ƙarya ko magabtan Kristi. Ƙari ga haka, ya nuna yadda za mu mai da hankali don kada su yaudare mu.”
Awake! Agusta
“Muna nuna wa mutane wani talifi da ya tattauna irin bayanin da ƙwayoyin halitta na jikinmu yake ɗauke da shi. [Ka nuna masa bangon talifin Awake! ɗin.] Mutane da yawa sun gaskata cewa waɗannan abubuwan sun wanzu farat ɗaya ne kawai, wasu kuma suna gani cewa halittar su aka yi. Mene ne ra ’ayinka? [Ka bari ya ba da amsa.] Wannan mujallar ta nuna wasu abubuwa da aka gano game da ƙwayoyin halitta masu ban al’ajabi da ya sa wasu ’yan kimiyya yin tunani cewa wataƙila akwai Mahalicci.”