Sanarwa
Littattafan da za a ba da a watannin Maris da Afrilu: Mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! Mayu da Yuni: Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko kuma ɗaya daga cikin warƙoƙin da kuke da su, alal misali, Za Ka So Ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin?, da kuma sababbin warƙoƙin da ke gaba: Mene Ne Ra’ayinka Game da Littafi Mai Tsarki?, Mene Ne Ra’ayinka Game da Nan Gaba?, Mene Ne Ke Kawo Farin Ciki a Iyali?, Wane Ne Ainihi Yake Iko da Duniya?, da kuma Wahala Za Ta Ƙare Kuwa?
Za a yi taron Tuna da Mutuwar Yesu a ranar Litinin 14 ga Afrilu, 2014. Idan Litinin ranar taron ikilisiyarku ne, za ku iya mai da taron zuwa wata rana dabam da ba a amfani da Majami’ar Mulkin a makon. Idan ba zai yiwu a gudanar da Taron Hidima a makon ba, mai tsara ayyukan rukunin dattawa zai iya shirya yadda za a ba da jawaban da suka shafi ikilisiyarku a wani lokaci dabam a wannan watan.
Jigon jawabi ga jama’a da mai kula da da’ira zai bayar somawa daga watan Maris 2014 shi ne, “Za Mu Sami Ceto Daga Matsalolin Duniya.”