Rahotannin Wa’azi
Muna farin cikin sanar da ku cewa mun sami sabon ƙoli a adadin masu shela da ya kai 351,205 a watan Agusta, 2013. Ƙari ga haka, mun sami sababbin ƙoli a adadin mutane da suka halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu da ya kai 715,888 da kuma mutane da muka yi nazari da su da suka kai 813,775. Yawan waɗanda da suka halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu a shekara ta 2013 ya fi na shekara ta 2012 da mutane 42,624. Hakika, muna ganin tabbaci cewa Jehobah yana ci gaba da yi ma wannan aikin albarka.