Ka Kāre Lamirinka
1. Mene ne jigon taro na musamman na shekara ta 2013, kuma mene ne manufar taron?
1 A kowace rana, muna fuskantar yanayi dabam-dabam da za su iya ɓata lamirinmu. Shi ya sa aka tsara taro na musamman da za a soma a watan Fabrairu na shekara ta 2013, da wannan jigon: “Ka Kāre Lamirinka.” (1 Tim. 1:19) An shirya taron ne don a taimaka mana mu mai da hankali sosai ga yadda muke amfani da wannan kyautar lamiri da Mahaliccinmu ya ba mu.
2. Waɗanne tambayoyi masu muhimmanci ne za a ba da amsoshinsu a taron?
2 Ku Mai da Hankali ga Waɗannan Darussan: Wannan taron zai amsa waɗannan muhimman tambayoyi bakwai game da lamiri:
• Mene ne zai iya gurɓata lamirinmu?
• Ta yaya za mu horar da lamirinmu?
• Ta yaya za mu wanke kanmu daga ɗaukan alhakin dukan mutane?
• Idan muna yin tunani a kan ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma muna aikata su, mene ne hakan zai bayyana game da halinmu?
• Idan ya zo ga al’amuran da ba su saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba, ta yaya za mu guji ɓata wa mutane rai?
• Matasa, ta yaya za ku yi tsayin daka sa’ad da mutane suka matsa muku ku yi wani abin da Allah ya haramta?
• Wane albarka ne waɗanda suke bin lamirin da ruhu mai tsarki yake yi wa ja-gora suke samu?
3. Ta yaya za mu amfana daga taron?
3 Jehobah zai iya taimaka mana mu yi tsayayya da Shaiɗan don kada ya ɓata lamirinmu. Ubanmu na sama mai ƙaunarmu yana amfani da Kalmarsa da kuma ƙungiyarsa wajen gaya mana cewa: “Wannan ita ce hanya, ku bi ta.” (Isha. 30:21) Wannan taron ɗaya ne daga cikin hanyoyin da Jehobah yake mana ja-gora. Saboda haka, ku yi shiri sosai don ku kasance a taron daga farko har zuwa ƙarshe. Yayin da kuke wurin taron, ku kasa kunne sosai kuma ku yi la’akari da yadda za ku yi amfani da darussan da za ku koya. Ku tattauna abubuwan da kuka koya a matsayin iyali bayan taron. Yin amfani da darussan da za mu koya zai ƙarfafa mu mu ci gaba da kasancewa da “lamiri mai kyau,” kuma zai taimaka mana mu guje wa sha’awoyin duniya da Shaiɗan yake amfani da su don ya ɓata dangantakarmu da Jehobah.—1 Bit. 3:16.