Sanarwa
◼ Littattafan da za a ba da a watan Fabrairu: Asirin Farinciki Na Iyali da Ka Kusaci Jehovah. Maris: Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ku yi ƙoƙarin soma nazarin Littafi Mai Tsarki a ziyara ta farko. Afrilu da Mayu: Mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! A inda ake son saƙonmu, ku ba da warƙar nan Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin? kuma ku yi ƙoƙarin soma nazarin Littafi Mai Tsarki da masu gida. Sa’ad da kuke koma ziyara wurin waɗanda suka halarci Tuna Rasuwar Yesu ko kuma wasu ayyuka da suka shafi bautarmu ga Allah amma ba sa tarayya da ikilisiyar sosai, ku mai da hankali ga soma nazari da su ta wajen yin amfani da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
◼ Jigon jawabi na musamman da za a ba da a makon da ake Tuna Rasuwar Yesu shi ne: “Ya Kusa Ne Fiye da Yadda Kuke Zato?”
◼ Duk sa’ad da kuke shirin tafiya zuwa ƙasar da ba ta cikin rahoto na shekarar hidima na kwanan nan ko kuma babu adireshin ƙasar a Hidimarmu Ta Mulki ta Fabrairu, don Allah ku tuntuɓi ofishin reshe da ke ƙasarku don su gaya muku abin da ya kamata ku yi ko kuma bayani na musamman da kuke bukatar ku bi. Wataƙila a ƙasar an hana yin wasu ayyuka na wa’azin Mulki. (Mat. 10:16) A wasu ƙasashe wataƙila ba zai dace ba baƙi su nemi Shaidun Jehobah ko kuma ikilisiyoyi. Za a iya ba ka wasu bayanai game da yin wa’azi idan ka samu zarafi ko kuma ba da littattafai. Bin ja-gorar da aka ba ka zai kāre ka daga matsaloli ko kuma kāre wa’azin Mulki a ƙasar da ka je ziyara.—1 Kor. 14:33, 40.