Bitar Makarantar Hidima ta Allah
Za a amsa waɗannan tambayoyi na gaba a Makarantar Hidima ta Allah a makon 28 ga Fabrairu, 2011. Mai kula da makaranta zai yi bita ta minti 20 daga abubuwan da aka tattauna a makonnin 3 ga Janairu zuwa 28 ga Fabrairu, 2011.
1. Wane aiki ne Hezekiya ya soma a farkon sarautarsa, kuma yaya za mu iya yin koyi da shi a yau? (2 Laba. 29:16-18) [w09 6/15 shafi na 9 sakin layi na 13]
2. Wane darasi mai kyau ne yake cikin 2 Labarbaru 34:1-3? [w05 12/1 shafi na 31 sakin layi na 5]
3. Ta yaya Ezra 3:1-6 ya goyi bayan bayanin da ke cikin Nassosi cewa kangon shekara 70 na Urushalima ta ƙare a kan lokaci? [w06 1/1 shafi na 9 sakin layi na 6]
4. Me ya sa Ezra ya yi mamaki sa’ad da ya ji game da auratayya da mutanen ƙasar? (Ezra 9:1-3) [w06 1/1 shafi na 10 sakin layi na 3]
5. Wane halin “hakiman,” ne ya kamata mu guje wa? (Neh. 3:5) [w06 2/1 shafi na 29 sakin layi na 1]
6. Ta yaya Gwamna Nehemiya misali ne mai kyau ga dattawan Kiristoci? (Neh. 5:14-19) [w06 2/1 shafi na 29 sakin layi na 4]
7. Kamar Isra’ilawa a zamanin Nehemiya, ta yaya za mu iya guji yin ƙyaliya da “gidan Allahnmu”? (Neh. 10:32-39) [w98 11/1 shafi na 16 sakin layi na 12]
8. Yin tunani a kan tafarkin Nehemiya zai motsa mu mu yi wa kanmu waɗanne tambayoyi? (Neh. 13:31) [w96 10/1 shafi na 14 sakin layi na 3]
9. Shin Esther ta yi lalata da Sarki Ahasuerus ne? (Esther 2:14-17) [w06 3/1 shafi na 30 sakin layi na 1]
10. Me ya sa Mordekai ya ƙi ya rusuna wa Haman? (Esther 3:2, 4) [w06 3/1 shafi na 30 sakin layi na 2]