Bitar Makarantar Hidima ta Allah
Za a amsa waɗannan tambayoyi na gaba a Makarantar Hidima ta Allah a makon 22 ga Fabrairu, 2010. Mai kula da makaranta zai yi bita ta minti 20 daga abubuwan da aka tattauna a makonnin 4 ga Janairu zuwa 22 ga Fabrairu, 2010.
1. Shin baban Ibrahim, Tera, mai bautar gumaka ne? (Josh. 24:2) [w04-HA 12/1 shafi na 7 sakin layi na 1]
2. Menene ya motsa Joshua ya furta abin da ya ce a Joshua 24:14, 15, kuma yaya ya kamata hakan ya shafe mu? [w08-HA 5/15 shafuffuka na 17-18 sakin layi na 4-6]
3. A wace hanya ɗaya ce masu bautar Baal da kuma salon bautarsu ta zama tarko ga Isra’ilawa kuma ta rinjaye su? (Alƙa. 2:3) [w08-HA 2/15 shafi na 27 sakin layi na 2-3]
4. Wane darasi ne za mu iya koya daga yadda Ehud ya yi amfani da takobinsa da gaba gaɗi? (Alƙa. 3:21) [w05-HA 3/1 shafi na 29 sakin layi na 3]
5. Wane darasi ne za mu iya koya daga Gidiyon da mutanensa ɗari uku? (Alƙa. 7:6) [w05-HA 3/1 shafi na 29 sakin layi na 7]
6. A wace hanya ce ran Jehobah ya “ɓaci saboda azabar Isra’ila”? (Alƙa. 10:16) [cl-HA shafi na 254 zuwa 255 sakin layi na 10 zuwa 11]
7. Shin Jephthah ya yi tunanin yin hadayar mutum ne sa’ad da yake yin alkawarinsa? (Alƙa. 11:30, 31) [w05-HA 3/1 shafi na 29 sakin layi na 11]
8. Idan “kowa yana ta yin yadda ya ga dama,” hakan zai jawo rashin jituwa ne? (Alƙa. 17:6-20) [w05-E 3/15 shafi na 30 sakin layi na 17]
9. Ta yaya za mu amfana don fahimtar ayyukan Samson waɗanda aka bayyana a Alƙalawa 16:3? [w04-HA 11/1 shafi na 15 sakin layi na 7 zuwa 8]
10. Me ya sa Jehobah ya ƙyale ƙabilar Biliyaminu ta fatattake sauran ƙabilun sau biyu, duk da yake tana bukatar horo? (Alƙa. 20:17-48) [w05-HA 3/1 shafi na 30 sakin layi na 20]