Abin da Ke Ciki
MAKON 1-7 GA OKTOBA, 2018
3 Ka San Gaskiyar Lamarin Kuwa?
MAKON 8-14 GA OKTOBA, 2018
8 Kada Ku Shari’anta Mutane Bisa Abin da Kuka Gani
A talifi na farko, an tattauna ƙalubalen da za mu iya fuskanta yayin da muke so mu san gaskiyar wani lamari. An kuma tattauna ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su iya taimaka mana mu san ko wani batu gaskiya ne ko a’a. A talifi na biyu kuma, an tattauna hanyoyi uku da mutane suke shari’anta wasu bisa abin da ake gani da ido. Ƙari ga haka, talifin ya nuna yadda za mu bi da mutane yadda ya dace.
13 Tarihi—Na Ƙudurta Cewa Ba Zan Karaya Ba
MAKON 15-21 GA OKTOBA, 2018
18 Masu Karimci Suna Farin Ciki
MAKON 22-28 GA OKTOBA, 2018
23 Ku Riƙa Yin Aiki da Jehobah Kowace Rana
Jehobah ya halicci mutane su riƙa yin farin ciki kuma su ji daɗin rayuwa. Muna farin cikin ganin yadda ayyukanmu suke sa a cim ma nufin Jehobah. A waɗannan talifofin, za mu tattauna yadda za mu iya yin aiki tare da Jehobah kullum da kuma yadda za mu amfana idan muna yin karimci a hanyoyi dabam-dabam.