Abin da Ke Ciki
3 Sun Ba da Kansu da Yardar Rai—A Myanmar
MAKON 3-9 GA SATUMBA, 2018
7 Wane ne Kake So Ya Amince da Kai?
A yau, mutane da yawa suna son mutanen duniyar nan su amince da su. A wannan talifin, za mu tattauna dalilan da suka sa ya kamata mu riƙa mai da hankali wajen samun amincewar Jehobah. Za mu kuma tattauna yadda Jehobah yake yin hakan a hanyoyin da ba mu yi zato ba a wasu lokuta.
MAKON 10-16 GA SATUMBA, 2018
12 Kana Zuba Ido ga Jehobah Kuwa?
A wannan talifin, za mu tattauna dalilin da ya sa Musa ya rasa gatansa na shigan Ƙasar Alkawari. Za mu kuma ga yadda za mu guji yin irin kuskuren da Musa ya yi.
MAKON 17-23 GA SATUMBA, 2018
MAKON 24-30 GA SATUMBA, 2018
Jehobah ne ya halicci dukanmu. Saboda haka, muna bukatar mu riƙa bauta wa shi kaɗai. Amma akwai wasu mutanen da suka yi da’awar bauta wa Allah yayin da suke yin abin da bai dace ba. A talifi na farko, za mu koyi darasi mai muhimmanci daga labarin Kayinu da Sulemanu da Musa da kuma Haruna. A talifi na biyu kuma, za mu tattauna hanyoyin da za mu nuna godiya ga Jehobah don gatan da muke da shi na zama bayinsa.
27 Ka Riƙa Jin Tausayin “Dukan Mutane”
30 Yadda Za Ka Sa Nazarin Littafi Mai Tsarki Ya Ƙara Daɗi da Kuma Inganci