Abin da Ke Ciki
MAKON 6-12 GA AGUSTA, 2018
3 ‘Mulkina Ba Na Duniya Ba Ne’
MAKON 13-19 GA AGUSTA, 2018
8 Mu Zama Tsintsiya Maɗaurinki Ɗaya Kamar Jehobah da Yesu
Batun siyasa da ƙabilanci da kuma wasu abubuwa sun raba kan mutane a zamanin Yesu. A waɗannan talifofi biyu, za mu tattauna yadda Yesu ya koya wa mabiyansa su riƙa kasancewa da haɗin kai kuma su daina nuna wariya da ke raba kan mutane. Za mu kuma ga yadda misalinsu zai iya motsa mu mu yi koyi da su.
13 Da Ya Sami Tagomashin Allah
MAKON 20-26 GA AGUSTA, 2018
16 Ka Bar Dokokin Allah da Kuma Ƙa’idodinsa Su Ja-gorance Ka
Idan muna so lamirinmu ya riƙa yi mana ja-goranci, dole ne mu koyar da shi. Jehobah ya tanadar mana da dokoki da kuma ƙa’idodi don su taimaka mana mu yi abubuwan da ke faranta masa rai. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu iya yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kullum a rayuwarmu.
MAKON 27 GA AGUSTA, 2018–2 GA SATUMBA, 2018
21 “Bari Ku Zama Masu Haske” Don Ku Ɗaukaka Jehobah
Yesu ya ƙarfafa almajiransa cewa su sa haskensu ya haskaka don su ɗaukaka Allah. Wannan talifin yana ɗauke da shawarwarin da idan mun bi su, ‘za mu zama masu haske.’
26 Tarihi—Na Sami Ƙarfafa Duk da Matsalolina
32 Ka Tuna?