Abin da Ke Ciki
MAKON 4-10 GA YUNI, 2018
3 Yadda Za Mu Sami ’Yanci na Gaske
MAKON 11-17 GA YUNI, 2018
8 Ku Bauta wa Jehobah, Allah Mai Ba da ’Yanci na Gaske
Mutane a faɗin duniya suna neman samun ƙarin ’yanci. Yaya ya kamata Kiristoci su ɗauki samun ’yanci? A waɗannan talifofi biyu, za a tattauna ma’anar ’yanci na gaske da yadda za a same shi da kuma yadda za mu yi amfani da shi don mu amfane kanmu kuma mu taimaka ma wasu. Ban da haka ma, za mu koya yadda za mu ɗaukaka Jehobah, Allahn da zai sa mu sami ’yanci na gaske.
13 Dattawa da Bayi Masu Hidima—Ku Bi Misalin Timoti
MAKON 18-24 GA YUNI, 2018
15 Mu Yi Koyi da Jehobah—Allahn da Ke Ƙarfafa Mu
MAKON 25 GA YUNI, 2018–1 GA YULI, 2018
20 Mu “Ƙara” Ƙwazo Wajen Ƙarfafa Juna
A waɗannan talifofin za mu koyi yadda Jehobah yake ƙarfafa bayinsa da kuma yadda suka bi misalinsa ta wurin ƙarfafa wasu. Za mu kuma ga abin da ya sa muke bukatar mu ƙarfafa juna yanzu fiye da dā.
MAKON 2-8 GA YULI, 2018
25 Yara da Matasa, Ku Kafa Maƙasudai a Bautarku
Yara da matasa suna farin ciki idan suka mai da hankali ga faranta wa Jehobah rai. Wannan talifin ya nuna dalilan da suka sa ya dace yara da matasa su kafa maƙasudai a hidimarsu ga Jehobah. Ƙari ga haka, za su ga dalilin da ya sa ya kamata su sa yin wa’azi a kan gaba a rayuwarsu.