Abin Da Ke Ciki
3 Sun ba da Kansu da Yardar Rai—A Madagaska
MAKON 26 GA FABRAIRU, 2018–4 GA MARIS, 2018
7 ‘Yana Ba da Ƙarfi ga Masu Kasala’
Mene ne za mu yi idan muna fusantar matsaloli sosai a rayuwa? A wannan talifin, za a tattauna jigonmu na shekara ta 2018 da kuma dalilin da ya sa za mu ba Jehobah damar ƙarfafa mu da kuma yadda zai yi hakan.
MAKON 5-11 GA MARIS, 2018
12 Taron Tuna da Mutuwar Yesu na Kawo Haɗin Kai
Za a Tuna da Mutuwar Kristi a ranar Asabar, 31 ga Maris, 2018. Ta yaya za mu shirya don wannan a yanzu? Ta yaya za mu amfana idan muka halarci taron tuna da mutuwar kuma ta yaya taron yake sa bayin Jehobah a ko’ina su kasance da haɗin kai? Za a sami amsar a wannan talifin.
MAKON 12-18 GA MARIS, 2018
17 Me Za Mu Iya Ba Wanda Yake da Kome?
Jehobah ne ya ba mu dukan abubuwan da muke da shi. Amma, har ila yana bukatar mu yi amfani da kuɗinmu don mu tallafa wa ƙungiyarsa. A wannan talifin, za mu tattauna dalilin da ya sa ya dace mu yi amfani da dukiyarmu don mu ɗaukaka Jehobah da kuma amfanin yin hakan.
MAKON 19-25 GA MARIS, 2018
22 Nuna Wace Irin Ƙauna Ce Ke Sa Mu Farin Ciki?
MAKON 26 GA MARIS, 2018–1 GA AFRILU, 2018
27 Za Ku Ga Bambancin da Ke Tsakanin Mutane
A talifi na farko, za a tattauna yadda mutum yake farin ciki sosai don yana ƙaunar Allah ba irin ƙauna da mutane suke nunawa a wannan “kwanaki na ƙarshe” ba. (2 Tim. 3:1) A talifi na biyu, za a tattauna yadda halayen mutane na kwanaki na ƙarshe ya yi dabam da na bayin Allah.
32 Ka Sani?