Abin Da Ke Ciki
MAKON 25 GA SATUMBA, 2017–1 GA OKTOBA, 2017
3 Kana Shirye Ka Jira Jehobah da Haƙuri?
MAKON 2-8 GA OKTOBA, 2017
8 Salama ta Allah ta Fi Ganewar Ɗan Adam
A talifi na farko, za mu bincika abin da ya sa ya kamata mu jira Jehobah. Za a kuma bincika yadda misalan mutanen dā za su iya taimaka mana mu riƙa haƙuri. A talifi na biyu, za a nuna yadda Jehobah zai yi abubuwa masu ban mamaki ta wajen cim ma abubuwan da ba mu taɓa tsammani ba. Hakan zai sa mu dogara gare shi don ya ɗau mataki a madadinmu.
13 Tarihi—Na Sami Albarka Sosai don Na Jimre da Tsanantawa
MAKON 9-15 GA OKTOBA, 2017
17 Yadda Za Mu Kawar da Halin Banza
MAKON 16-22 GA OKTOBA, 2017
22 Ka Ɗauki Sabon Hali kuma Ka Ci gaba da Hakan
A talifi na farko, an bayyana abin da yake nufi mu tuɓe halinmu na dā da kuma dalilin da ya sa yin hakan yake da gaggawa yanzu. Za a kuma bincika abin da za mu yi don mu kawar da halinmu na dā da ba shi da kyau. A talifi na biyu, za a nuna halaye da yawa da mutum zai koya, kuma za a bayyana yadda za mu riƙa nuna waɗannan halayen a rayuwarmu da kuma sa’ad da muke wa’azi.