Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w17 Mayu pp. 31-32
  • “Muna Kara Kwazo da Kauna Fiye da Dā”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Muna Kara Kwazo da Kauna Fiye da Dā”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
w17 Mayu pp. 31-32
Majami’ar da ke cike da mutane a babban taro da aka yi a Cedar Point, Ohio a shekara ta 1922

DAGA TARIHINMU

“Muna Ƙara Ƙwazo da Ƙauna Fiye da Dā”

KO DA yake ana zafi sosai, a ranar Jumma’a ga watan Satumba ta shekara ta 1922, mutane 8,000 sun taru a wani babban daƙin taro. Mai kujera ya sanar cewa mutane za su iya fita idan suna so, amma ba za a yarda su shigo ba.

An soma taron da sashen da ’yan’uwa suke rera waƙoƙi, bayan haka sai ɗan’uwa Joseph F. Rutherford ya hau kan dakalin magana. Yawancin mutane sun zauna suna jiran abin da zai faru. Amma kaɗan daga cikinsu suna ta zagayawa don irin zafin da ake yi. Sai mai jawabin ya ce musu su zauna don su saurari jawabin. Shin da aka fara jawabin mutane sun ga labulen da aka rataye a sama ne?

Ɗan’uwa Rutherford ya yi jawabi a kan jigon nan “Mulkin sama ya kusa.” Ya yi awa ɗaya da rabi yana ba da jawabi da babbar murya a kan yadda annabawa suka yi wa’azi da gaba gaɗi game da Mulkin Allah. Da ya kusan kammala jawabin, sai ya ce, “Kun gaskata cewa Sarki na daraja ya soma sarauta?” Sai waɗanda suka halarci taron suka amsa da babbar murya suka ce: “E!”

Bayan haka, sai Ɗan’uwa Rutherford ya ce da babbar murya: “Sai ku koma fili, ya ku ’ya’yan Allah maɗaukaki!” Ya kuma ce: “Duba, Sarkin yana sarauta! Ku ne ma’aikatansa. Saboda haka, ku yi shela, ku yi shela, ku yi shelar sarkin da kuma Mulkin.”

A wannan lokacin ne aka daga labulen kuma jama’a suka ga jigon nan: “Ku Yi Shelar Sarkin da Kuma Mulkin.”

Ray Bopp da yake wurin a lokacin ya ce: “Jama’a sun yi mamaki ba kaɗan ba.” Anna Gardner ta kwatanta abin da ya faru ta ce: “Jama’a sun yi tafi sosai har daƙin ya girgiza.” Fred Twarosh ya ce: “Dukan jama’a sun tashi tsaye.” Evangelos Scouffas ma ya ce: “Kamar wani abu ne ya dāga mu duka daga kan kujerunmu kuma muka tashi tsaye muna kukan murna.”

Yawancin jama’a da suka halarci taron suna yin wa’azin Mulkin Allah. Duk da haka, jawabin ya ƙarfafa su ci gaba da yin hakan. Ethel Bennecoff ta ce Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun koma gidajensu da aniyar “ci gaba da wa’azi da kuma ƙaunar mutane da ƙwazo.” Odessa Tuck da a lokacin take da shekara 18 ta koma gida da aniyar ba da amsar tambayar da Jehobah ya yi cewa ‘Wa zan aika?’ Ta ce: “Ban san inda zan yi wa’azi ko yadda zan yi shi ko kuma abin da zan faɗa ba. Amma abin da na sani shi ne na so in zama kamar Ishaya wanda ya ce: ‘Ga ni; ka aike ni.’” (Isha. 6:⁠8) Ralph Leffler ya ce: “A wannan ranar ne aka soma shelar Mulkin sosai da ake yi a ko’ina a duniya yanzu.”

Babu shakka, shi ya sa ba za a taɓa mantawa da taron nan da aka yi a shekara ta 1922 a Cedar Point, Ohio a tarihin Shaidun Jehobah ba. George Gangas ya ce: “Wannan taron ya taimaka mini in ga muhimmancin halartan manyan taro.” Kuma tun daga lokacin, yana ganin bai taɓa fasa halartan manyan taro ba. Julia Wilcox ta ce: “A duk lokacin da aka ambaci taron Cedar Point a shekara ta 1922 a littattafanmu, ina farin ciki sosai. A kullum ina cewa, ‘Na gode wa Jehobah don yadda ya sa na halarci wannan babban taron da aka yi.’”

Wataƙila mu ma muna da wasu manyan taron da muka halarta da ya motsa zuciyarmu kuma ya sa muka kasance da ƙwazon yin wa’azi da kuma ƙaunar Allahnmu da kuma Sarkinsa. Idan muna yin tunani a kan taron a kullum, mu ma za mu iya cewa, “Mun gode wa Jehobah don yadda ya sa muka halarci wannan babban taron da aka yi.”

Wasu Harufa da ba a San Ma’anarsu Ba

An rubuta harufan nan “ADV” (a Turanci) a ko’ina a kan itatuwa da gidaje, har a kan takardar tsarin ayyuka na taron. Waɗannan alamun sun sa waɗanda suka halarci taron tunani ko mene ne hakan yake nufi.a

Edith Brenisen ta ce: “An saka fararen katuna a kan alluna da ƙofofi a inda aka rubuta harufan nan ADV a manyan baƙaƙe. Mun tambayi abin da waɗannan harufan suke nufi, amma ba wanda ya sani, ko kuma idan sun sani ba za su gaya mana ba.”

a Har ila ba a gan ainihin waɗannan harufa na dā ba. Kuma ’yan’uwa da suke aiki a sashen da ake adana kayan Tarihi sun nemi ainihin hotunan waɗannan harufan da aka saka musu kala ba, amma ba su gani ba.

An Amsa Addu’arsu ta Wata Hanya Mai Ban Mamaki

Arthur da Nellie Claus sun isa wurin da za a yi taron da wuri don su sami wurin zama mai kyau. Arthur ya ce: “Na mai da hankali sosai ga abin da ake faɗa a taron.” Amma, nan da nan sai ya soma jin ciwon ciki. Ya yi jinkirin fita daga ɗakin taron don ya san ba zai iya sake dawowa ba. Wani ya tambaye shi, “Me ya sa kake son ka fita a wannan lokacin?” Amma Arthur ya san cewa ya zama dole ne ya fita.

Sa’ad da Arthur ya dawo, sai ya ji ana tafi sosai a cikin ɗakin taron. Ya nemi wani wuri a waje da zai iya jin abin da ake yi a ciki, sai ya gano wani wurin da zai iya hawa zuwa rufin daƙin, kuma tsawonsa ya kai wajen ƙafa 16. Ƙari ga haka, ya hau ta wundo da ke saman gidan.

Arthur ya ga wasu ’yan’uwa suna cikin wata damuwa, suna kallon mai jawabin. An umurce su su yanke igiyoyi da yawa a lokaci ɗaya don mutane su ga wani rubutu da aka yi a wani labule. Amma kafin a yanke igiyoyin a lokaci ɗaya, suna bukatar wuƙaƙe da yawa. Shin Arthur yana da wata wuƙa ne a cikin aljihunsa? E. Sai Arthur da sauran suka jira a ba su alama don su yanke igiyar. Sa’ad da Ɗan’uwa Rutherford ya ce “Ku yi Shela!” a lokaci na biyu, sai dukansu suka yanke igiyoyin da suka riƙe labulen.

Waɗanda suke wurin sun faɗi yadda aka buɗe labulen mai kala uku. An zana hoton Yesu a tsakiyar labulen.

Da aka gama taron sai ’yan’uwa suka gaya wa Arthur cewa sun hau lada zuwa rufin gidan kuma aka ɗauke ladar. Saboda haka, ba yadda za su sauko su nemo wasu wuƙaƙe, sai suka yi addu’a ga Jehobah ya tura musu wani ɗan’uwa da zai taimaka musu da wuƙa. Waɗannan ’yan’uwan suna da tabbaci cewa Jehobah ya amsa addu’arsu a hanya mai ban mamaki.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba