Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp17 Na 4 p. 3
  • Tambaya Mai Ban Mamaki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambaya Mai Ban Mamaki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Rai da Mutuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
wp17 Na 4 p. 3
Wata mata ta kuna kyandir kuma tana amfani da rosary tana addu’a

Kusan dukan addinai sun yi imani cewa kurwar ’yan Adam ba ta mutuwa

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ME LITTAFI MAI TSARKI YA CE GAME DA RAI DA MUTUWA?

Shin Muna Ci gaba da Rayuwa Bayan Mun Mutu?

MUTANE suna da ra’ayoyi da yawa game da rayuwar ʼyan Adam da kuma mutuwa. Wasu sun yi imani cewa bayan sun mutu, za su ci gaba da rayuwa a wani wuri ko kuma su zama wani abu dabam. Wasu sun ce za a sake haifansu don su sake rayuwa. Wasu kuma sun ce mutuwa ce ƙarshen ʼyan Adam.

Wataƙila abin da ka yi imani da shi dabam ne saboda al’adarka. Tun da mutane suna da ra’ayoyi dabam-dabam a kan wannan batun, shin da akwai abin da zai taimaka mana mu san gaskiyar al’amarin?

Limaman addinai sun daɗe sosai suna koya wa mutane cewa wani abu a jikin mutum yana ci gaba da rayuwa bayan mutuwa. Kusan dukan addinai kamar Kiristoci da Hindu da Yahudawa da Musulmai da dai sauransu sun yi imani da hakan. Amma ’yan Buddha sun yi imani cewa za a ci gaba da haifan mutum har sai tunaninsa ko kuma motsin ransa ya koma wani wurin da ake kira Nirvana.

Mutane suna saka wa kabarin wani nasu abinci

Waɗannan koyarwar sun sa yawancin mutane a duniya sun yi imani cewa idan mutum ya mutu, zai ci gaba da rayuwa a wani wuri. Mutane da yawa sun yi imani cewa mutuwa tana da muhimmanci sosai a rayuwar ’yan Adam. Sun kuma ce mutuwa nufin Allah ne. Amma mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da wannan batun? Don Allah, ka karanta talifi na gaba. Abin da ke ciki yana da ban mamaki.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba