Abin Da Ke Ciki
MAKON 30 GA MAYU, 2016–5 GA YUNI, 2016
3 Allah Yana Albarkar Waɗanda Suka Kasance da Aminci
A wannan talifin, an tattauna abin da ya taimaka wa Jephthah da ‘yarsa su kasance da aminci duk da mawuyacin yanayi da suka fuskanta. Za mu koyi abin da ya sa ya dace mu yi duk wani sadaukarwa don Jehobah ya amince da mu.
MAKON 6-12 GA YUNI, 2016
9 ‘Bari Haƙuri Ya Cika Aikinsa’
Wajibi ne mu kasance masu haƙuri har ƙarshen wannan zamani idan muna so mu sami kyautar rai na har abada. A wannan talifin, an tattauna wasu abubuwa huɗu da za su taimaka mana mu jimre da kuma misalai guda uku na waɗanda suka jimre da aminci. Ƙari ga haka, an bayyana yadda kowannenmu zai sa haƙuri ya cika aikinsa.
MAKON 13-19 GA YUNI, 2016
15 Me Ya Sa Ya Kamata Mu Riƙa Halartan Taro don Ibada?
Akwai abubuwa da yawa da za su iya sa halartan taro a kai a kai ya kasance da wuya a gare mu. An tattauna wasu abubuwa masu ban ƙarfafa a wannan talifin da za su taimaka mana mu riƙa halartan taro a kai a kai. Ƙari ga haka, an bayyana yadda halartan taro yake amfanar mu da kuma faranta wa Jehobah rai.
MAKON 20-26 GA YUNI, 2016
21 Ku Nisanta Kanku Daga Harkokin Wannan Duniyar da Babu Haɗin Kai
Gwamnatoci da yawa a yau suna barin mu mu yi zaman ‘yan ba ruwanmu, amma ya kamata mu san cewa yanayi zai iya canjawa kuma su ƙi yin haka yayin da ƙarshen yake gabatowa. A wannan talifin, za mu tattauna abubuwa huɗu da za su taimaka mana mu kasance da aminci ga Jehobah a wannan yanayin.
27 TARIHI—Budurwai Masu Zaman Zuhudu Sun Zama ‘Yan’uwanmu
31 Shin Wa’azin da Kake Yi Yana Kamar Raɓa Ne?